An yankewa alkalin kotun Najeriya hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari

An yankewa alkalin kotun Najeriya hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari

Wata babbar kotun Najeriya dake Maitama a Abuja ta yankewa wani alkalin kotun majistare, Mohammed Balogun, daurin shekaru uku a gidan yari bayan samun sa da laifin neman na goro domin canja hukuncin shari'a.

Saidai alkalin kotun, Ishaq Bello, da ya yanke masa hukuncin ya bashi zabin biyan tarar N500,00.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin jami'an gwamnati ICPC) ce ta gurfanar da Balogun bisa tuhumar sa da laifuka guda biyu da suka hada a neman na goro.

Da yake yanke masa hukunci, mai shari'a Bello, ya ce wannan shine karo na farko da wanda ake tuhmar ya taba gurfana gaban kotu da sunan aikata laifi kuma ya amsa laifinsa ba tare da wahalar da shari'a ba.

An yankewa alkalin kotun Najeriya hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari

An yankewa alkalin kotun Najeriya hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari

Sannan ya kara da cewar, Balogun na fama da matsananciyar damuwa saboda iyalinsa sun kaurace masa tun faruwar lamarin.

"Abinda ya yi ba daidai bane a matsayinsa na mutumin da hukuma ta damkawa amana da ikon tabbatar da gaskiya da adalci a tsakanin jama'a. Neman ko karbar cin hanci ya sabawa ka'idar aiki kuma cin amana ne.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta bayyana inda dumbin kudi da kadarorin da aka kwato suke

"Tunda wannan shine karo na farko da aka taba gurfanar da kai a gaban kotu, na yanke maka hukuncin daurin shekaru a kurkuku ko kuma ka biya tarar N500,000."

Hukumar ICPC ta gurfanar da Balogun bayan ya nemi nemi wani mutum, Dakta Isidore Nnadi, ya biya shi N100,00 kafin ya yi hukunci a kan wasu korafi guda biyu da ya shigar kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel