Matsalar tsaro: An sake kashe mutane biyar wani hari da yan bindiga suka kai kauyen Kadarko a jihar Nassarwa

Matsalar tsaro: An sake kashe mutane biyar wani hari da yan bindiga suka kai kauyen Kadarko a jihar Nassarwa

- Daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu mutane 12 sun sara ranzu sakamakon harin da ake kaimu

- Kura ta lafa bayan da yan sanda suka isa yankin da aka kaiwa sabon harin

Rundunar yan sanda reshen jihar Nassarawa ta tabbatar da kai hari ga kauyen Kadarko dake karamara hukumar Obi a ranar Talata, kuma har mutane biyar sun rasa rayukansu.

Da yake jawabi, jami’in hulda da jama’a na rundunar Mr Kennedy Idirisu ya shaidawa manema labarai cewa, maharani sun kai harin ne da tsakar dare kan duk wanda sukai arba da shi.

KU KARANTA: Zaben 2019: Limamin Birtaniyya yayi wa Buhari alkawarin addu’a samun sa’a

Kennedy Idirisu yace, rundunar yan sanda ta aike da isassun jami’anta domin tabbatar da an magance kurar wanda kuma kwalliya ta biya kudin sabulu.

Matsalar tsaro: An sake kasha mutane biyar wani hari da yan bindiga suka kai kauyen Kadarko a jihar Nassarwa

Matsalar tsaro: An sake kasha mutane biyar wani hari da yan bindiga suka kai kauyen Kadarko a jihar Nassarwa

Ya kara da cewa, yanzu haka jami’ansu sunyi nasarar cafke mutane uku da suke zargi da hannu wajen kai wancan farmaki. Kuma kwamishinan yan sanda na jihar Alhaji Ahmed Bello, yana kan hanyarsa ta zuwa domin gane kansa yadda lamarin yake da kuma jajantawa al’umar yankin.

wani mazaunin yankin da yayi magana da manema labarai ya bayyana cewa, kafadar wani saurayi mai shekaru 17 aka fara yankewa da rana, kuma suna zargin makiyaya ne suka kai musu harin.

Kana daga bisani maharan suka biyo dare gami da afka musu suna sara da harbinsu babu ji ba gani. ”Hatta sansanin yan gudun hijira basu kyale shi ba, wanda haka yayi sandiyyar jima wasu da yawa ciwo sakamakon gudun ceton rai da suke yi musamman mata da kananan yara.” Inji wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta.

Dama dai kauyen na Kadarko Mahara sun taba kai masa hari a ranar 29 ga watan Janairu na cikin wannan shekarar. Inda har mutane bakwai suka sheka har lahira.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel