Atiku ne kadai dan takarar da zai iya kada Buhari a zaben 2019 - Kungiya

Atiku ne kadai dan takarar da zai iya kada Buhari a zaben 2019 - Kungiya

- Kungiyar siyasa ta Atiku Grassroots Ambassadors na Najeriya tace tsaohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar shine kadai dan takarar da zai iya kada Buhari a zaben 2019

- Shugaban kungiyar MistaFerguson Okapala ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da NAN a ranar 10 ga watan Afirilu a garin Awka

- Ferguson yace abunda yanzu kadai muke bukata shine jam’iyyar PDP suyi abunda ya kamata su tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar su

Wata kungiyar siyasa ta Atiku Grassroots Ambassadors na Najeriya tace tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar shine kadai dan takarar da zai iya kada shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019, mai zuwa.

Shugaban kungiyar Mr. Ferguson Okapala ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da NAN a ranar 10 ga watan Afirilu a garin Awka.

Atiku ne kadai dan takarar da zai iya kada Buhari a zaben 2019

Atiku ne kadai dan takarar da zai iya kada Buhari a zaben 2019

Ferguson yace abunda yanzu kadai muke bukata shine jam’iyyar PDP suyi abunda ya kamata su tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar su, saboda shi kadai ne yake da cancanta, da damar da zai iya fuskantar Buhari.

KU KARANTA KUMA: Wanda akewa zargin fashi da makami yace yanawa wani dan Sanda aiki ne

Okpala yace Buhari nada damar sake tsayawa takara, amma dai jam’iyyar adawa ya zama dole su fitar da dan takara wanda zai kawo mata kuri’u masu yawa a zabe mai zuwa na 2019.

Okpala yace mulki dai na Allah ne, saboda haka kwazo shine zai nuna wanda ya kamata a zaba lokacin zaben 2019, kuma muna da tabbashin cewa Atiku yana da wannan kwazon wanda zaisa a zabeshi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel