Wanda akewa zargin fashi da makami yace yanawa wani dan Sanda aiki ne

Wanda akewa zargin fashi da makami yace yanawa wani dan Sanda aiki ne

- Wani matashi dan shekara 21 Akeem Popoola yace wani speto na ‘Yan Sanda ke amfani dashi wurin kwacewa mutane kayayyakinsu

- Matashin ya bayyan sunan Speton shine Festus wanda akafi sani da Ijaya, wanda yace ya kai kimanin wata hudu yana masa aiki

- Matashin wanda ke aikin kahinta yana tsare a Ofishin ‘Yan Sanda na Agbado jihar Ogun

Wani matashi dan shekara 21 Akeem Popoola yace wani speto na ‘Yan Sanda ke amfani dashi wurin kwacewa mutane kayayyakinsu.

Matashin ya bayyan sunan Speton shine Festus wanda akafi sani da Ijaya, wanda yace ya kai kimanin wata hudu yana masa aiki, kafin aka kamashi.

Matashin wanda ke aikin kahinta yana tsare a Ofishin ‘Yan Sanda na Agbado jihar Ogun, ana zarginsa da fashi da kuma sata. An samu katifa da kayan kidi a hannunsa, a lokacin da aka kamashi a ranar 6 ga watan Afirilu a kauyen Giwa dake garin Agbado.

Wanda akewa zargin fashi da makami yace yanawa wani dan Sanda aiki ne

Wanda akewa zargin fashi da makami yace yanawa wani dan Sanda aiki ne

Punch Metro sun ruwaito cewa bayan satar da yakeyi yana kuma karbar wayoyi daga hannun Speto Festus yana siyarwa. Byana lokacin kadan kuma Festus da abokanansa Abbey da Aluko, sais u kama wama wanda ya siyarwa wayar suce ya siya kayan sata.

KU KARANTA KUMA: Buhari na kan aikin ceton Najeriya ne - Zangon Daura

Mai magana da yawun hukumar ‘Yan Sanda na jihar Ogun DSP Muyiwa Adejobi, yace hukumar na ta kokarin gano Festus da abokanansa. Kuma an mayar da lamarin binciken zuwa Anti-Robery Squad.

Mai magana da yawun hukumar ‘Yan Sanda na jihar Legas, SP Dolapo Badmos, ta karyata zance, inda tace basu da wani ma’aikaci mai suna Festus ko wanda ake kira Ijaya a Ofishinsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel