Zaben 2019: Limamin Birtaniyya yayi wa Buhari alkawarin addu’a samun sa’a

Zaben 2019: Limamin Birtaniyya yayi wa Buhari alkawarin addu’a samun sa’a

- Babban Shehin Katolika na Ingila ya sa wa tazarcen Buhari albarka

- Shugaba Buhari dai ya bayyana cewa zai zarce kafin ya bar Najeriya

- Fasto Welby na Birtaniyya yace za su dafawa Shugaban dai da addu’a

Jiya ne mu ka samu labari cewa babban Limamin cocin Angilika na Duniya watau Justin Welby ya bayyana cewa za su taya Shugaban kasa Buhari da addu’ar domin ganin ya samu sa’a a zaben Najeriya mai zuwa na 2019.

Zaben 2019: Limamin Birtaniyya yayi wa Buhari alkawarin addu’a samun sa’a

Justin Welby zai yi wa Buhari addu’a game da 2019

Bishof Justin Welby ya bayyanawa Shugaban kasa Buhari cewa ya ji lokacin da ya bayyana cewa zai sake takara a zabe mai zuwa don haka yace za su sa shi addu’a domin Ubangiji ya dafa masa a matsayin su na Shehunnai.

KU KARANTA:

Justin Welby wanda Aminin Shugaban kasar na Najeriya ne ya kai masa ziyara ne a jiya a gidan Shugaban kasar da ke Ingila. Duk da alakar da ke tsakanin su, Faston yace ba za su goyi bayan kowa a zabe mai zuwa ba

Babban Limamin ya nuna cewa a matsayin sa na Malamin addini ba za su nuna goyon bayan su ga kowa ba sai dai za su iya taimakawa Shugaba Buhari da addu’o’i domin ganin Ubangiji ya ba sa nasara a zaben da za ayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel