Wata Mata ta buƙaci saki sakamakon Mijinta mai yawan jima'i ta Dubura

Wata Mata ta buƙaci saki sakamakon Mijinta mai yawan jima'i ta Dubura

A ranar Alhamis din da ta gabata ne wata uwargida mai sunan Asma'u Sulaiman, ta roki Kotun Shari'ar Musulunci dake zamanta a unguwar Magajin Gari ta jihar Kaduna, akan ta raba ta da mijin ta sakamakon yawan buƙatar saduwa da ita ta Dubura.

Malama Asma'u ta kuma shaidawa kotun cewa, mijin na ta Nura Ahmad, ya na cin zarafin ta tare da yi ma ta kazafin keta ma sa haddi na aure.

A kalaman ta, "akwai lokacin da na yi kaura zuwa gidan iyaye na sakamakon wata sa'insa da ta shiga tsakanin mu, dawowa ta ke da wuya sai ya zarge ni da zubar da ciki wanda kuma ba gaskiya ba ne."

Rahotanni da sanadin shafin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, a halin yanzu dai wannan mata tana neman Kotu ta zartar da adalci cikin lamarin sakamakon gazawar ta na ci gaba da jure wannan cin kashi da kuma gudun kamuwa da wata cuta ta hanyar saduwa ta Dubura.

KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga sun kashe mutane 10 a jihar Benuwe

Legit.ng ta fahimci cewa, mijin na ta ya karyata wannan zargi da tuhumce-tuhumce na matar sa.

Mai shari'a Mallam Musa Sa'ad, ya nemi Asma'u akan gabatar da shaidar wanna zargin da za su tsaya mata a matsayin hujja, inda ta ce tabbas akwai shaidu in banda ta lamarin saduwa.

Alkalin kotun ya daga sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Afrilu domin bayar da dama ta gabatar da shaidu kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel