Buhari na kan aikin ceton Najeriya ne - Zangon Daura

Buhari na kan aikin ceton Najeriya ne - Zangon Daura

- Tsohon ministan gona, Alhaji Sani Zangon Daura, yace ya kamata ‘yan Najeriya su goyawa Buhari baya saboda yana kan aikin ceton Najeriya

- Zangon Daura yace wadanda ke adawa da komawar Buhari kujerar shugaban kasa karo na biyu suna da damar yin haka

- Yayi kira ga ‘yan Najeriya dasu tattaru su sake marawa Buhari baya ya sake zama shugaban kasa saboda ba yanayi don kansa bane

Tsohon ministan gona, Alhaji Sani Zangon Daura, yace ya kamata ‘yan Najeriya su goyawa Buhari baya saboda yana kan aikin ceton Najeriya.

Zangon Daura yace wadanda ke adawa da komawar Buhari kujerar shugaban kasa karo na biyu suna da damar yin haka,kuma yawancinsu a tsorace suke saboda suna da wani laifi da suke gudun a gano.

Buhari na kan aikin ceton Najeriya ne - Zangon Daura

Buhari na kan aikin ceton Najeriya ne - Zangon Daura

Zangon Daura yayi kira ga ‘yan Najeriya dasu tattaru su sake marawa Buhari baya ya sake zama shugaban kasa saboda ba yanayi don kansa bane ko dan yaci wata riba, ko kuma don ya saci kudaden al’umma bane.

KU KARANTA KUMA: Femi Adesina ya bayyana bangaren da shugaba Buhari ke da rauni

Buhari yayi hakane don ya ceto Najeriya daga halin da ta shiga, kamar yanda kafin hawansa mulki kowa ya sani mutane saida ya zama basu iya zuwa masallaci ko coci ko makabarta ko biki cikin kwanciyar hankali ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel