‘Yan kwadago sun nemi a maida albashin Ma’aikatan Gwamnati N65, 000

‘Yan kwadago sun nemi a maida albashin Ma’aikatan Gwamnati N65, 000

- ‘Yan kwadago su na fafutuka a kara mafi karancin albashin Gwamnati

- Har yanzu dai akwai Ma’aikatan da ke karbar N18, 000 kacal a duk wata

- Shugaban ‘yan kwadago na kasar yace ya kamata a rika biyan N65,000

Labari ya zo mana cewa Kungiyar NLC ta ‘Yan ‘Yan kwadagon Najeriya da kuma TUC ta ‘Yan kasuwan kasar sun nemi a kara mafi karancin albashin da Ma’aikata a Najeriya za su iya karba daga Gwamnati N18, 000.

‘Yan kwadago sun nemi a maida albashin Ma’aikatan Gwamnati N65, 000

Ma'aikata na nema a kara albashin Ma’aikata a Najeriya

Manyan Kungiyoyin Ma’aikatan Kasar su na bukatar Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta maida albashin Ma’aikata zuwa akalla N65, 500 a wata. ‘Yan kwadagon sun ci ma wannan mataki ne bayan dogon nazari da su kayi.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya ba Lauyan da ke kare Zakzaky a Kotu mukami

‘Yan kwadagon sun yi la’akari ne da wasu abubuwa 4 wanda su ka hada da albashin sauran kasashen Afrika sannan kuma an duba tsadar rayuwa da muhalli a Najeriya. Ma’aikatan sun ce N18, 000 tayi kadan a wannan marra.

Kwamared Ayuba Wabba wanda shi ne Shugaban Kungiyar kwadago na kasar ya bayyana wannan a Birnin Tarayya. Sai dai har yanzu rokon na su bai samu shiga ba tukuna a Gwamnatin domin sai kwamitin da aka nada sun zauna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel