Femi Adesina ya bayyana bangaren da shugaba Buhari ke da rauni

Femi Adesina ya bayyana bangaren da shugaba Buhari ke da rauni

- Kakakin shugaban kasa yace ya tarar da Buhari a masaukinsa na London yana shirye shiryen tarbar Archbishop Justin Welby

- Adesina yace a wurin jira na baki na tarar da Ambassador George Adesola Oguntade, tsohon Alkalin kotun koli ta Najeriya

- Femi yace baya sun shiga Adesola ya fadawa shugaba Buhari cewa yana hanyar zuwa ganin jikansa ne a makaranta ya nuna rashi jin dadin dawo dashi da akayi, ya kuma bashi hakuri akan hakan

Adesina yace ya tarar da Buhari a masaukinsa na London, yana shirye shiryen tarbar Archbishop Justin Welby zai kawo masa ziyara.

Adesina yace a wurin jira na baki na tarar da Ambassador George Adesola Oguntade, tsohon Alkalin kotun koli ta Najeriya, mai shekaru 78.

Yace bayan sun shiga Adesola ya fadawa shugaba Buhari cewa yana hanyar zuwa ganin jikansa Mofoluwaso Oguntade, a makaranta ya gama karatun digiri na biyu. Buhari ya nuna rashi jin dadin dawo dashi da akayi, ya kuma bashi hakuri akan hakan, ya kumace zaiyi magana jikan nasa.

KU KARANTA KUMA: Bukar yayi kokarin samun amincewar majalissa akan gina Poly ta tarayya a jihar Katsina kafin rasuwarsa - Sanatoci

Ambassador Oguntade ya dauka wayarsa ya kira jikan nasa, babban maikaci a Najeriya. Shugaban kasar ya nuna masa jin dadinsa, ya tayashi murna, ya kuma bashi hakuri game da yanda ya hana kakansa zuwa wurinsa cikin rashin sani.

Byayan haka shugaban kasa ya bukaci katin taya murna wanda kakan nasa ya siyo masa, ya karba ya sake rubuta cewa “ina sake tayaka murna kuma ina baka hakuri game da hana kakanka zuwa wurinka”.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel