'Yan uwan Nnamdi Kanu sun buƙaci gawar sa domin binne ta

'Yan uwan Nnamdi Kanu sun buƙaci gawar sa domin binne ta

Iyalai da 'yan uwan Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB ta masu fafutikar kafa yankin Biyafara, sun nemi gwamnatin tarayya ta ba su gawar dan uwan su domin shirya ta tare kuma da kai ta ga sanyawa a makwancin ta.

A halin yanzu dai 'yan uwan Kanu sun yarda cewa tuni ya riga mu gidan gaskiya a yayin da rundunar dakarun sojin kasa ta yi yunkurin kwantar da tarzoma ta tayar da kayar baya akan kafa yankin Biyafara tun a shekarar da ta gabata.

Mai magana da yawun iyali da 'yan uwa, Emma Kanu, ya shaidawa manema labarai na Daily Sun cewa, su na buƙatar gwamnatin tarayya da ta ba su gawar dan uwan su ta Nnamdi domin binneta ta hanyar da ta dace.

'Yan uwan Nnamdi Kanu sun buƙaci gawar sa domin binne ta

'Yan uwan Nnamdi Kanu sun buƙaci gawar sa domin binne ta

Emma ya bayyana cewa, tun lokacin da shugaban IPOB ya ɓace a bara yayin da rundunar sojin kasa ta kai simame gidan sa, su ka fara fargaba akan rayuwarsa.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya za a gina Gadar Kasa ta N4bn a jihar Kano - Ganduje

A kalaman sa, "a yanzu da muka samu rahoton ajali ya cimma sa, ya kamata gwamnatin tarayya ta ba mu gawar sa cikin gaggawa domin daukacin al'ummar kabilar Ibo ta yi binnewa irin ta hanyar dace da kuma cancanta kasancewar sa jinin su."

Emma ya kara da cewa, ko da kuwa shugaban kungiyar IPOB a halin yanzu ba ya cikin masu gwagwarmayar Biafara, hakan ba zai kawo tasku cikin shawarar kungiyar da daukacin al'ummar Ibo na cimma manufarta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel