'Yan kabilar Ijaw sun bukaci ayi afuwa ga shugaban tsagerun Neja Delta

'Yan kabilar Ijaw sun bukaci ayi afuwa ga shugaban tsagerun Neja Delta

- Kungiyar matasan kabilar Ijaw sun aike da wata sakon gagawa ga gwamnatin tarayya

- Kungiyar tana son gwamnatin ta janye dukkan tuhume-tuhumen da ake yiwa Ekpemupolo wanda akafi sani da Tompolo

- Tompolo dai yayi layyar zana tun bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya dare karagar mulki

Kungiyar matasan kabilar Ijaw, 'Ijaw Youth Council' (IYC) tayi kira ga gwamnatin tarayya ta janye dukkan tuhume-tuhumen da ake yiwa tsohon shugaban yankin Neja-Deltan mai suna Cif Government Ekpemupolo wanda akafi sani da Tompolo

Kungiyar ta IYC tayi wannan kira ne cikin wata sanarwa da shugaban Kungiyar, Eric Omare ya aike wa 'yan jarida a ranar Laraba 11 ga watan Afrilu.

Matasan kabilar Ijaw sun roki gwamnati tayiwa shugaban tsagerun Neja Delta afuwa

Matasan kabilar Ijaw sun roki gwamnati tayiwa shugaban tsagerun Neja Delta afuwa

DUBA WANNAN: Ta rinchabe a Majalisa yayinda Sanatan PDP yace shugaba Buhari ya gaza

Wani bangare na sanarwan yace, "Kungiyar IYC tana bukatar gwamnati ta janye tuhumar da take yiwa Cif Government Ekpemupolo dangane da siyar da filin wucin gadi na Jami'ar Maritime."

Duk da haka kungiyar ta yabawa shugaba Muhammadu Buhari bisa yadda yayi tsayin daka har aka fara gudanar karatu da sauran horaswa a jami'ar ta Maritime.

Kungiyar kuma ta bukaci gwamnatin tarayya ta janyo hankalin yan kwangilar domin su cigaba da gudanar da ayyukan gyare-gyare a matsugunin jami'ar na dundundun domin su koma can din.

Sun kuma koka kan yadda har yanzu gwamnatin bata zartar da bukatun da kungiyar ta gabatar ba a yayin wata taron sulhu don dakatar da kai hare-haren kungiyar Neja Delta Avengers, musamman bukatarsu ne dawo da hedkwatan kampanonin man fetur yankin na Neja Delta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel