Za'a bayyanawa al'umma kasafin kudin Majalisa na 2018

Za'a bayyanawa al'umma kasafin kudin Majalisa na 2018

A jiya Laraba ne shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan yace majalisar zata bayyanawa al'ummar Najeriya kasafin kudin majalisar na shekarar 2018 saboda kowa yasan adadin kudaden da majalisar ke kashewa.

Lawan ya furta hakan ne a lokacin da yake jawabi ga manema labarai akan sabbin tsarin majalisar wanda aka bullo da su saboda a kara bawa al'umman Najeriya daman sanin abubuwan dake faruwa a cikin Majalisar.

Za'a bayyanawa al'umma kasafin kudin Majalisa na 2018

Za'a bayyanawa al'umma kasafin kudin Majalisa na 2018

Lawan ne ke jagorantar kwamiti na musamman da aka kafa don gudanar da wani taron na musamman wanda akayi wa lakabi fa 'Open Week Event' wanda za'a fara daga ranar 25 zuwa 29 na watan Yuni a harabar majalisar dake babban birnin tarayya Abuja.

DUBA WANNAN: Kofa a bude take ga duk mai son tsayawa takarar shugabancin kasa a APC

Lawan ya misalta shirin a matsayin wata abu da ke tasowa inda ya kara da cewa sauran kasashen duniya tuni su n rungumi wannan tsarin na janyo al'umma kusa da masu mulki saboda a fayace musu yadda komai ke tafiya.

Lawan yace irin wannan shirin zai kara yarda da amana tsakanin yan majalisar da al'ummar da suke wakilta kuma zai rage cin hanci da rashawa tunda masu mulki sun san cewa al'umma na sane da abinda ke faruwa a majalisar.

Abubuwan da za'a gudanar yayin taron na kwanaki hudu sun hada da amsa tambayoyi da tattaunawa tsakanin al'umma, kungiyoyi da yan majalisar da kuma yawan bude ido a harabar majalisar don a ilmantar da al'umma kan yadda majalisar ke gudanar da ayyukansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel