Babu zabe da na'ura a shekarar 2019 - Hukumar zabe (INEC)

Babu zabe da na'ura a shekarar 2019 - Hukumar zabe (INEC)

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ce babu maganar gudanar da zabe ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa a shekarar 2019.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya sanar da haka ranar Talata a karshen wani taro na kwanaki uku da hukumar ta gudanar a kan dama da kalubalen amfani da fasaha a zabe.

A kalamansa: "Ina son sanar da jama'a cewar maganar gudanar da zaben shekarar 2019 ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa ba abu ne mai yiwuwa ba duk da cewar zamu yi amfani da fasaha wajen gudanar da zabukan."

Babu zabe da na'ura a shekarar 2019 - Hukumar zabe (INEC)

Babu zabe da na'ura a shekarar 2019 - Hukumar zabe (INEC)

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta bayyana inda dumbin kudi da kadarorin da aka kwato suke

Farfesa Mahmoud ya kara da cewa amfani da fasaha wajen gudanar da zabe ba iya hukumar INEC ya shafa ba, ya shafi hatta masu kada kuri'a wadanda yawancinsu ba zasu iya amfani da na'ura wajen kada kuri'a yayin zabe ba.

Sannan ya cigaba da cewar hukumar INEC zata karbi sakamakon zabuka kai tsaye ta hanyar amfani da na'urori da za a yi amfani da su wajen tantance adadin mutanen da suka kada kuri'a duk da cewar hukumar zata raba fom din EC8A da ake rubuta sakamakon zabe a kansa.

Farfesa Mahmoud ya ce tuni suka gudanar da gwajin karbar sakamakon zabe kai tsaye ta amfani da sabuwar fasahar a zaben gwamna da aka yi a jihar Anambra.

Kalubalen da hukumar INEC ke fuskanta shine yadda zata tabbatar da tsaro ga na'urorin yayin zabe, a cewar Farfesa Mahmoud.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel