Trump zai fara hukunta masu amfani da shafin yanar gizo suna safarar mata

Trump zai fara hukunta masu amfani da shafin yanar gizo suna safarar mata

- Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu akan wata dokar da zata hukunta masu safarar mata a yanar gizo

- Dokar dai anyi ta ne domin ta taimaka gurin hukunta masu safarar mutane a yayin da za a bukaci wanda abin ya faru dashi da ya bayyana adireshin yanar gizon da suka taimaka wajen faruwar al'amarin

Trump zai fara hukunta masu amfani da shafin yanar gizo suna safarar mata

Trump zai fara hukunta masu amfani da shafin yanar gizo suna safarar mata

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu akan wata dokar da zata hukunta masu safarar mata a yanar gizo.

Dokar dai anyi ta ne domin ta taimaka gurin hukunta masu safarar mutane a yayin da za a bukaci wanda abin ya faru dashi da ya bayyana adireshin yanar gizon da suka taimaka wajen faruwar al'amarin.

DUBA WANNAN: An kama wani Sanata da digirin bogi

Sa hannun ya faru ne a birnin Washington domin karfafa bincike akan kafofin sadarwa na fasaha wadanda da yawansu suke karya doka.

Wasu daga cikin kafofin sadarwar sun nuna tsoron su akan sa hannun inda suke ganin hakan zai iya zama barazana gare su.

Sanatan Republican, Rob Portman, mataimaki a majalisar gurin sa hannu a dokar yace "wannan rana ce mai dumbin tarihi a yaki da safarar mutane domin jima'i ta yanar gizo da kuma nasara ga wadanda suka taba fadawa tarkon,kuma aka danne musu hakkinsu na adalcin da ya kamata.

A ranar litinin ne karar da akayi ta shafin Backpage.com wacce akayi sakamakon zargin da ake yiwa shafin na zama na biyu a kafofin sadarwar yanar gizon da suke safarar mutane suna kai su wasu wuraren domin a dinga saduwa dasu ana biyan su.

Trump, wanda ake tsammanin zai sa hannun ya ki ansa tambayoyin manema labarai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel