Kofa a bude take ga duk mai son tsayawa takarar shugabancin kasa a APC

Kofa a bude take ga duk mai son tsayawa takarar shugabancin kasa a APC

- Jam'iyyar APC ta bayyana cewa kofa a bude take ga duk mai sha'awar fitowa takarar shugabancin kasa ya bayyana ra'ayinsa

- Jam'iyyar tace kundin tsarin mulkin jam'iyyar bai haramtawa sauran yan jam'iyyar fitowa ba

- Duk da haka, Sakataren yadda labarai na jam'iyyar, Bolaji Abdullahi yace zai dace a bawa shugaba Buhari dama ya karasa ayyukan daya faro

A jiya ne sakataren yadda labarai na jam'iyyar APC, Malam Bolaji Abdullahi yace a halin yanzu shuguba Muhammadu Buhari ne kawai ya bayyana ra'ayinsa na tsayawa takaran shugabancin kasa a zaben 2019 amma hakan bai haramtawa wasu yan jam'iyyar fitowa ba.

Abdullahi ya fadi hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a Ilorin na jihar Kwara. Ya kara da cewa bayyana ra'ayin na shugaba Muhammadu Buhari ya sanya jam'iyyar kara mayar da hankali don tunkarar zaben na 2019.

Kofa a bude take ga duk mai son tsayawa takarar shugabancin kasa a APC

Kofa a bude take ga duk mai son tsayawa takarar shugabancin kasa a APC

DUBA WANNAN: Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da wani tsohon Kwamishina a jihar Imo

Ya cigaba da cewa duk da cewa mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar sunyi farin ciki da matsayar na shugaba Buhari, kudin tsarin mulkin jam'iyyar ya bawa sauran yan jam'iyyar ikon fitowa takarar duk da cewa daga baya jam'iyyar zata iya daukan matakin daya dace.

Abdullahi yace ba'ayi adalci ba idan akace shugaba Muhammadu Buhari ne kawai dan takarar da jam'iyyar ta tsayar duk da cewa a halin yanzu shi kadai ne ya bayyana ra'ayinsa, sai dai yana ganin ayyukan da shugaba Buhari ya fara suna da matukar muhimmanci ga kasa kuma zai dace a bashi damar ya karasa.

Yace shekaru hudu sunyi kadan ga gwamnatin ta kammala dukkan ayyukan da ta fara, hakan yasa yake ganin abinda yafi zama alheri ga yan Najeriya shine su bawa shugaba Buhari dama ya karasa aikin daya dauko.

Daga karshe yace, jam'iyyar APC ba kamar PDP bane inda a zaben 2015 suka hana kowa ikon tsayawa takara idan ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel