Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da wani tsohon Kwamishina a jihar Imo

Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da wani tsohon Kwamishina a jihar Imo

Rahotanni daga jaridar Vanguard sun bayyana cewa wasu yan bindiga da ake tunanin masu garkuwa da mutane sun sace tsohon kwamishinan al'adu da yawon shakatawa na jihar Imo, Engr. Alex Ogwazuo.

Yan bindigan sun sace shi ne a karshen makon daya wuce a babban birnin jihar Imo, Owerri. Tsohon kwamishinan wanda Gwamna Rochas ya sallama daga aiki yana hanyarsa na zuwa wani buki ne inda yan bindigan suka tare shi kuma suka tafi tashi.

Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da wani tsohon Kwamishina

Masu garkuwa da mutane sunyi awon gaba da wani tsohon Kwamishina

Yan bindigan sun sace shi ne a motar sa kuma har yanzu ba'a ji duriyarsu ba.

Kafin sallamarsa daga aiki, tsohon kwamishinan kuma yayi aiki a matsayin Ciyaman na Cibiyar kula da jihohi masu samar da man fetur na jihar Imo.

DUBA WANNAN: An gurfanar da wata a kotu bisa zargin kashe dan makwabciyarta ta hanyar tsafi

A wata labarin kuma, wasu yan bindigan sun sace dan wani dan kasuwan, dan asalin kasar Syria da ke zaune a jihar Kano inda suka harbe mutumin, Ahmed Abu Areeda kafin suka sace dan nasa, Muhammed Ahmed.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, abin takaicin ya faru ne yayin da mutumin ya kammala aiki kuma ya tafi daukar motarsa a harabar kungiyar bayar da agaji na Red Cross da ke Kano inda ya saba ajiye motarsa.

Kakakin hukumar Yan sanda na jihar Kano ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya kara da cewa jami'an hukumar sun fara gudanar da bincike kan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel