Bukar yayi kokarin samun amincewar majalissa akan gina Poly ta tarayya a jihar Katsina kafin rasuwarsa - Sanatoci

Bukar yayi kokarin samun amincewar majalissa akan gina Poly ta tarayya a jihar Katsina kafin rasuwarsa - Sanatoci

- Sanatoci sun tina yanda marigayi Sanata Bukar yayi kokarin kawo muhawara a majalissa game da gina makarantar Poly ta tarayya a jihar Katsina

- Sanatocin sun bayyana hakane lokacin da suke gudanar da taron girmamawa ga marigayi Bukar wanda ya rasu a ranar laraba data gabata

- Bukar ya jagoranci muhawara akan kirkira gurin koyon gini da bincike akan hanyoyi a Najeriya da kuma kirkira makarantar Poly ta tarayya a jihar Katsina

A jiya ne Sanatoci suka tina da yanda marigayi Sanata Bukar (APC-Katsina) yayi kokarin kawo muhawara a majalissa game da gina makarantar Poly ta tarayya a jihar Katsina, duk da rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sanatocin sun bayyana hakane, a ranar 8 ga watan Maris, lokacin da suke gudanar da taron girmamawa ga marigayi Bukar wanda ya rasu yana da shekaru 63, a ranar Laraba data gabata.

Bukar ya jagoranci muhawara akan kirkira gurin koyon gini da bincike akan hanyoyi a Najeriya da kuma kirkira makarantar Poly ta tarayya a garin Daura dake jihar Katsina.

Bukar yayi kokarin samun amincewar majalissa akan gina Poly ta tarayya a jihar Katsina kafin rasuwarsa - Sanatoci

Bukar yayi kokarin samun amincewar majalissa akan gina Poly ta tarayya a jihar Katsina kafin rasuwarsa - Sanatoci

Mataimakin shugaban majalissa Ike Ekweremadu ya tina da yanda Bukar ya bukaci a saurari muhawarar da ya gabatarwa majalissar tun 7 ga watan Maris. Amma “bamu samu sauraronta ba sai washe gari inda bai sake dawowa ba har mutuwarsa”, inji shi.

KU KARANTA KUMA: 'Danyen man da ake hakowa a Najeriya kowace rana ya ragu da ganga 82, 000

Haka kuma shugaban wadanda aka rinjaya a majalissar Godswill Akpabio yace, lokacin da yake gabatar da muhawarar, bamu san cewa bankwana mukeyi da Bukar ba.

Ahmed Lawan jigon majalissa ya bukaci a gaggauta iyar da muhawarar da Bukar ya gabatar, yace “Yanda muhawarar zata kasance da sunansa”. Sai shugaban majalissa Bukola Saraki yace zasuyi jimamin Bukar saboda halayensa na kirki da kuma abubuwan cigaba da yake kawowa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel