Kwangilolin da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya sa hannu a taron FEC na jiya

Kwangilolin da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo ya sa hannu a taron FEC na jiya

A jiya ne aka yi taron Majalisar zartarwa na Ministocin Najeriya wanda Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci taron a dalilin rashin Shugaban kasa Buhari.

Kwangilolin da Mataimakin Shugaban kasa Osinbajoo ya sa hannu a taron FEC na jiya

Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo a wajen taron Majalisar FEC

A zaman dai an cin ma matakai da yawa don haka ne mu ka kawo su a jere domin a san inda aka dosa. Daga cikin kwangilolin da aka bada dai akwai na aikin titi da kuma yasar ruwa da kuma gina Jami’ar Sojoji.

1. Kwangilar hanyoyi

A taron da Yemi Osinbajo ya ja ragama jiya, an amince da cewa za a gyara wasu hanyoyi 3 a kasar a kan kudi Naira Biliyan 47 kamar yadda Ministan ayyuka Babatunde Fashola ya bayyana. Ayyukan su ne na Titin Babban Lamba zuwa Shandam sai kuma hanyar Legas zuwa Ota sai titin Aba zuwa Fatakwal.

KU KARANTA: Yadda za ta kare da Shugaban kasa Buhari a zaben 2019

2. Yasar ruwan Warri

Haka kuma Ministan sufuri na kasar watau Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayyar tayi na’am da a kashe Naira Biliyan 13 wajen yasar tashan ruwan nan na Escavos da ke Garin Warri a Jihar Delta.

3. Jami’ar Sojoji

Gwamnatin Buhari ta kuma bada damar a gina Jami’ar Soji a Najeriya a Garin Biu a cikin Jihar Borno. Malam Adamu Adamu wanda shi ne Ministan ilmi na kasar ya bayyanawa manema labarai wannan a Birnin Tarayya Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel