Kwana yazo karshe: Wani dan jariri ya mutum bayan ya tunjuma cikin randar ruwa a dakin babarsa

Kwana yazo karshe: Wani dan jariri ya mutum bayan ya tunjuma cikin randar ruwa a dakin babarsa

An tsinci gawar wani dan jariri mai watanni takwas a Duniya, daga cikin wani randar ruwa dake ajiye a dakin mahaifiyarsa, dake garin Obakhavbaye na karamar hukumar Oredo, a jihar Edo.

Daily Trust ta ruwaito wani mazaunin garin ya shaida ma yan jaridu cewa dan jaririn mai suna Abdulaziz Abubakar Aji, ya bata ne da tsakar dare, inda aka nemi shi sama ko kasa aka rasa, zuwa safiya iyayen sun shaida ma makwabtansu lamarin, inda gaba daya aka dunguma aka shiga neman yaron.

KU KARANTA: Gimbiya sarautar mata: Manyan mata guda 10 da suka nuna bajinta a fannoni daban daban a Najeriya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ana cikin haka ne sai mahaifin ya shiga dakinsu da nufin debo ruwa cikin randar ruwan dakin, inda bude randar keda wuya sai ya ci karo da gawar yaro Abdulaziz.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa: “Mahaifiyar yaron ta shiga bayi ne da tsakar dare, inda bayan dawowarta ne ta nemi yaron nata ta rasa, don haka ake ganin ko ma waye ya kashe yaron nan, ya jefa cikin randar ne a lokacin da matar ta shiga bayi.”

Zuwa yanzu dai Yansanda sun yi awon gaba da iyayen yaron da kishiyar matar don fara gudanar da bincike, tare da gano yadda yaron ya gamu da ajalinsa, kamar yadda Kwamishinan Yansandan jihar Babatunde Kokuma ya bayyana, inda yace babu yadda za’a yi yaron ya fada ruwan da kansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel