An karkatar da Biliyan 1.6 ta hanyar kwangiloli a NEMA – Majalisa

An karkatar da Biliyan 1.6 ta hanyar kwangiloli a NEMA – Majalisa

- ‘Yan Majalisan Najeriya sun gano wata badakala da ake tafkawa a NEMA

- Majalisa ta gano cewa an karkatar Biliyan 1.5 a Hukumar da ke bada agaji

- Shugaban Hukumar ya bada kwangiloli ga kamfunan da ba su cancanta ba

Labari ya zo mana cewa wani kwamiti da ke lura da Hukumomin da ke shiryawa kwana-kwana a Majalisar Wakilan Tarayya sun gano cewa akwai wata badakala da ake tafkawa a Hukumar nan ta NEMA ta Kasar.

An karkatar da Biliyan 1.6 ta hanyar kwangiloli a NEMA – Majalisa

An karkatar wasu makudan kudi Hukumar NEMA a Najeriya

Kamar yadda Jaridar Premium Times ta rahoto, ‘Yan Majalisan kasar sun gano cewa an karkatar wasu makudan kudi da su ka haura Naira Tiriliya 1.5 a Hukumar NEMA wajen bada kwangilolin da ba su cancanta ba.

KU KARANTA: Wata mata ta nemi Mijin ta ya cika mata sadakin ta bayan ta haihu

A ka’ida dai sai kamfani yana da cikakken takardu na haraji da shaida sannan ake ba sa kwangila. Sai dai Hukumar ta NEMA mai bada agajin gaggawa ta bada kwangiloli ga Kamfanoni fiye da 200 da ya sabawa ka’ida.

Ana zargin cewa Mustafa Maihaja wanda shi ne Shugaban Hukumar bai yi bincike ba kafin ya bada kwangilolin. Bayan maganar haraji ma dai an sabawa dokar BPP na bada kwangiloli a Najerjiya inji Majalisar kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel