An kama wani Sanata da digirin bogi

An kama wani Sanata da digirin bogi

- Sanata mai wakiltar jihar Bayelsa ta yamma, Sanata Foster Ogola, an kama shi tsumu-tsumu da takardar kammala digiri ta karya, wadda ya alakanta ta da wata jami'a a Najeriya

- Da aka yi magana da daraktan yada labarai na hukumar kula da makarantun jami'a ta kasa, Ibrahim Yakasai, ya bayyanawa manema labarai shi bai ma taba jin sunan makarantar ba sai a ranar

An kama wani Sanata da digirin bogi

An kama wani Sanata da digirin bogi

Sanata mai wakiltar jihar Bayelsa ta yamma, Sanata Foster Ogola, an kama shi tsumu-tsumu da takardar kammala digiri ta karya, wadda ya alakanta ta da wata jami'a a Najeriya.

DUBA WANNAN: Dakarun Sojin Saman Najeriya sun fito da wani tsari na tallafawa sansanin 'yan gudun hijira da magunguna

Ya saka a shafin sa na intanet, inda ya ke nuna cewa ya gama digirin digirgir a wata jami'a, mai suna GMF Christian University. Sai dai kuma hukumar makarantun jami'a ta kasa, NUC ta nuna cewar bata yi wa jami'ar rijista ba. Inda shi kuma aka gano cewar ya mallaki nasa digirin digirgir din tub a shekarar 2012." Kamar yanda wani rahoto ya nuna.

Da aka yi magana da daraktan yada labarai na hukumar kula da makarantun jami'a ta kasa, Ibrahim Yakasai, ya bayyanawa manema labarai shi bai ma taba jin sunan makarantar ba sai a ranar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel