Babu wata bindiga ko makami da zai iya shiga jikina - inji wani dan kungiyar asiri

Babu wata bindiga ko makami da zai iya shiga jikina - inji wani dan kungiyar asiri

- Wani shugaban 'yan kungiyar asiri da hukumar 'yan sanda ta (RRS) shiyyar jihar Legas ta kama a Jakande Estate dake yankin Ajah karshen makon nan daya gabata, ya ce babu wata bindiga ko makami da zai iya bula jikinsa

Babu wata bindiga ko makami da zai iya shiga jikina - inji wani dan kungiyar asiri

Babu wata bindiga ko makami da zai iya shiga jikina - inji wani dan kungiyar asiri

Wani shugaban 'yan kungiyar asiri da hukumar 'yan sanda ta (RRS) shiyyar jihar Legas ta kama a Jakande Estate dake yankin Ajah karshen makon nan daya gabata, ya ce babu wata bindiga ko makami da zai iya bula jikinsa.

DUBA WANNAN: Sabbin bayanai daga hukumar kidaya: Yawan 'yan Najeriya ya kai mutum 200,000,000

An kama wanda ake zargin mai suna Andrew Awalebi, mai shekaru 35, an kama shi tare da abokan aikin nasa su uku a wata mashayar giya ranar Juma'ar nan da misalin karfe 8 na safe. 'Yan sandan sun kuma sake nasarar kama biyu daga cikin 'yan kungiyar washe garin ranar Asabar a wani Otal dake Ikorodu a birnin Legas, wanda suka hada da, Adegoke Adeleke mai shekaru 30, Kehinde Adebogun mai shekaru 31.

Awalebi dan asalin karamar hukumar Ilaje dake jihar Ondo, 'yan sandan sun samu nasarar kama shi da taimakon wani daga cikin 'yan kugiyar tasu mai suna Michael Thompson.

Shi dai Thompson an kama shi a daren da aka yi fashi da makami a babban filin wasanni na Surulere dake jihar. Awalebi ya bayyana cewar yana aiki da wani babban mai kudi a unguwar Lekki, ya kuma bayyana cewar yana samun naira 40,000 duk wata daga wurin masu sai da filaye, saboda kokarin da yake yi musu wurin kula da filayen su a yankin wurin.

Ya shaidawa masu binciken na shi cewar sai da aka shirya shi sosai a wani kauye Ijebu-Isiwo dake jihar Ogun da magunguna da baza su saka bindiga ko wani makami ya shiga jikin sa ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel