Cakwakiya: Bayan haihuwar yaya 2, wata Mata ta nemi Mijinta ya cika mata ragowar sadakinta, N13,000

Cakwakiya: Bayan haihuwar yaya 2, wata Mata ta nemi Mijinta ya cika mata ragowar sadakinta, N13,000

Wata uwargida mai suna Zuwaira Abdulaziz ta garzaya gaban wata Kotun shari’ar Musulunci, inda ta bukaci a kwato mata hakkinta daga wajen mijinta, bashin N13,000, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Uwargida Zuwaira ta tinkari Kotun ne dake zamanta a Magajin Gari na jihar Kaduna, inda ta bayyana mata cewar Maigidanta, Musa Dantsoho yaki ya cika mata ragowar bashin kudin sadakinta da take binsa, da suka kai naira dubu goma sha uku.

KU KARANTA: Masana Ilimin Kimiyya sun gano kasar Sifaniya na girgiza a duk lokacin da Messi ya ci Kwallo

Ta shaida ma Kotun cewar naira dubu bakwai kacal Dantsoho ya bata daga cikin naira dubu ashirin da suka amince ya biya a matsayin sadakinta tun kafin su yi aure, inda yace zai cika mata sauran ragowar kudin, amma har yanzu ya kasa cika alkawarinsa, duk da kuwa auren ya samar da yaya guda biyu.

Sai dai ta tabbatar ma Kotun cewar basu rubuta yarjejeniyar da ta shiga da Mijin nata ba, kuma bata taba shaida ma iyayenta sun yi hakan ba: “Ban fada ma iyayen cewar bai cika kudin sadakin nasa ba, saboda na yarda da shi, ashe bashi da mutunci ko na miskala zarratan.”

Daga nan kuma ta roki Kotun da ta bata damar mayar masa sadakin da ya biyata N7,000 don a tsinka igiyar auren dake tsakaninsu, matukar ba zai iya biyanta sauran kudinta ba. Sai dai gogan naku ya rantse cewar ya biyata cikon sadakinta tun tuni.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin, Alkali Dahiru Lawal ya kashe auren, sa’annan ya umarci Zuwaira ta mayar ma Musa Dantsoho da sadakin da yace ya biyata, N20,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel