Dakarun Sojin Saman Najeriya sun fito da wani tsari na tallafawa sansanin 'yan gudun hijira da magunguna

Dakarun Sojin Saman Najeriya sun fito da wani tsari na tallafawa sansanin 'yan gudun hijira da magunguna

- Sojojin saman Najeriya sun fito da wani tsari na bada tallafi ga sansanin yan'gudun hijira na garin Rann dake jihar Borno na kwanaki uku, wanda zai fara daga 10 ga watan Afirilu, zuwa 13 ga watan Afirilu. Shirin ya biyo bayan janyewar da kungiyoyin bada tallafin gaggawa ga 'yan gudun hijiran suka yi wato (NGO), hakan kuma ya biyo bayan tsanan ta hari da 'yan kungiyar Boko Haram suke yi a kwanan nan

Dakarun Sojin Saman Najeriya sun fito da wani tsari na tallafawa sansanin 'yan gudun hijira da magunguna

Dakarun Sojin Saman Najeriya sun fito da wani tsari na tallafawa sansanin 'yan gudun hijira da magunguna

Sojojin saman Najeriya sun fito da wani tsari na bada tallafi ga sansanin yan'gudun hijira na garin Rann dake jihar Borno na kwanaki uku, wanda zai fara daga 10 ga watan Afirilu, zuwa 13 ga watan Afirilu. Shirin ya biyo bayan janyewar da kungiyoyin bada tallafin gaggawa ga 'yan gudun hijiran suka yi wato (NGO), hakan kuma ya biyo bayan tsanan ta hari da 'yan kungiyar Boko Haram suke yi a kwanan nan.

DUBA WANNAN: Ku rage tsadar magani da ganin likita - Haj. Aisha Buhari ga asibibitoci da ba na gwamnati ba

Shugaban rundunar sojin saman na kasa, Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce hukumar karkashin jagorancin sa zata samarda magunguna daban daban, da kuma gidajen sauro wanda za a rabawa yan gudun hijirar. Tallafin dai zai iya taimakon sama da mutane 3,350 na yan'gudun hijiran bayan haka kuma kimanin mutane 40 zuwa 65 za a yi musu aikin idon.

A ranar farko, an dauki wanda suke cikin tsananin rashin lafiya a jirgi zuwa helkwatar sojin saman da ke garin Maiduguri. Yan gudun hijirar tara ne suka amfana da aikin tiyata, sai kuma mutane 8 da aka yiwa aikin tiyatar ido, wanda ko sisi ba a karba daga gurinsu ba.

Shugaban cibiyoyin kiwon lafiya na sojojin sama, Air Vice Marshal Saleh shinkafi, ya tabbatar da cewa taimakon magunguna da tiyata suna cikin aiyukan kyautatawar da sojojin saman zasuyi ma yan'gudun hijirar domin kalubalen da suke fuskanta ta fannin lafiya. Wasu daga cikin mutanen da suka samu taimakon suna mika godiyarsu ta yanda sojojin suka nuna musu kauna kuma suna kira ga sauran kungiyoyi da mutane dasu yi koyi da sojojin.

Shirin wanda ake tsammanin zai kwantar wa da yan gudun hijiran wadanda Boko Haram suka yi sanadiyyar barin gidajen su hankali. Haka zalika kokarin da sojojin saman sukayi gurin fada da yan'ta'addan, tare da wayar da kan yan gudun hijiran ya taka rawar gani gurin kwantar musu da hankali.

Idan ba mance ba sojojin sama sune akann gaba gurin aikin ceto a Arewa maso gabas fiyeda shekaru uku da suka wuce. Sojojin saman sun shirya shirin taimakon bada magunguna a Arewa maso gabas da kuma dukkannin sassa na kasar. Sojojin saman sun samarda asibitocin aikin gaggawa na yan gudun hijira, da kuma samar wa daliban firamare na yan gudun hijirar wurin karatu a yankin Dalori da Bama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel