Hukumar EFCC ta damke yan damfaran yanar gizo 14

Hukumar EFCC ta damke yan damfaran yanar gizo 14

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, shiyar jihar Legas, a ranan Talata, 10 ga watan Afrilu, 2018 ta damke yan damfaran yanar gizo 14.

Yan damfaran sune Abiola Kayode, Adeleye Adewale, Adeniyi Abiola, Favour Iruabo, Iyiola Olayemi, Lawal Remilekun and Martins Adetunji.

Sauran sune, Obafunsho Oladipupo Samson, Olaleye Bamilola Hassan, Oseni Ridwan, Peter Ayobami Samuel, Peter Toluwabori, Prince Jibril Dirisu da Richard Jerry John.

An damke wadannan yan damfaran ne a Badore, Ajah jihar Legas bisa ga rahoton da aka samu kan yadda suke rayuwa. An kwato manyan motoci da kwamfutoci daga hannayensu.

Hukumar EFCC ta damke yan damfaran yanar gizo 14

Hukumar EFCC ta damke yan damfaran yanar gizo 14

Hukumar za ta gurfanar da su a kotu muddin an karasa bincike a kansu.

KU KARANTA: Hukumar NAPTIP ta damke masu safarar mutane 8

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Jami’an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta yi ram da wasu yan damfaran yanar gizo 4 a ranan Asabar, 7 ga watan Afrilu 2018 a jihar Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel