Gwamna ya zubar da hawaye bayan rattaba hannu a kan kasafin kudi, karanta dalilinsa

Gwamna ya zubar da hawaye bayan rattaba hannu a kan kasafin kudi, karanta dalilinsa

Gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade, ya gaza rike hawayensa bayan rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2018.

Ayade ya rattaba hannu a kan kasafin kudi na tiriliyan N1.3tn a gaban majalisar jihar.

Gwamnan ya zubar da hawaye tare da bayyana cewar ya mika kasafin kudin ga ubangiji.

Ayade ya ce jihar Kuros Riba na bukatar irin wannan kasafin kudi kafin jihar ta iya fita daga kangin matsalolin rashin kayan more rayuwa da suka haddasa matsalolin zamantakewa a tsakanin kabilun jihar.

Gwamna ya zubar da hawaye bayan rattaba hannu a kan kasafin kudi, karanta dalilinsa

Gwamna Ben Ayade

Ayade ya bukaci jagororin al'umma da mutanen jihar da su tashi tsaye wajen kawo sabbin tunani da zasu canja halin da jihar ke ciki musamman ta fuskar tattalin arziki da jihar ta kasance koma baya.

DUBA WANNAN: Gasar zakarun Turai: Messi ya zargi kungiyar Manchester United a kan rashin nasarar kungiyar Barcelona a hannun Roma

Kazalika gwamnan ya bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu duk da karancin kudin shiga da jihar ke fama da shi.

A nasa bangaren, shugaban majalisar jihar Kuros Riba, John Gaul Lebo, ya bayyana goyon bayan majalisar ga gwamna Ayade tare da bayar da tabbacin saka ido a kan kasafin kudin jihar domin ribar jihar da mutanen ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel