Sabbin bayanai daga hukumar kidaya: Yawan 'yan Najeriya ya kai mutum 200,000,000

Sabbin bayanai daga hukumar kidaya: Yawan 'yan Najeriya ya kai mutum 200,000,000

- Yawan jama'a arziki ne ga kowacce kasa, muddin suna da ilimi da iya tunani

- Yawancin Najeriya, mazauna karkara ne, da matalauta da marasa ilimin zamani

- Yawan zai iya zama illa muddin arziki ya durkushe, ko aka yi fari

Sabbin bayanai: Yawan 'yan Najeriya ya kai mutum 200,000,000
Sabbin bayanai: Yawan 'yan Najeriya ya kai mutum 200,000,000

Hukumar Kidaya ta kasa, ta saki sabbin bayanai kan yawan 'yan Najeriya, bayan da ta kasa kidayar jama'a a shekarar 2016, kamar yadda aka shirya a baya, shekaru 10 kenan da kidayar a lokacin shugaba Obasanjo a 2006.

A sabuwar kidayar ta hasashe, wadda kan yi amffani da yawan jama'a, yawa-yawan haihuwarsu, mutuwarsu, auratayyarsu, da ma shige-da ficensu, hukumar ta ce yawan jama'ar kasar nan ya doshi miliyan 200, kuma babu alamar kakkautawa.

Yawan na jama'a albarka ce, amma fa ga kasar da ke da alkibla, ko Najeriya tana da wannan alkibla? Tukunna dai, rabin jama'arta talakawa ne, babu ilimi, yara akalla miliyan 20 suna almajirci, babu aikin yi, masu aikin yin basu da isasshen kudi.

Kasa ce da bata iya tabuka komai sai ta sayo komai daga waje, yawan masallatai da coci-coci ya fi yawan masana'antu da makarantu.

Anyi amanna cewa, idan kasar ta ruguje, ko gwamnatin tarayya ta kasa baiwa jihohi kudaden da take rabawa duk wata, jama'ar kasar zasu shiga halin haa'ulaa'i, domin dan kudin ne ake tallaawa jihohin da kanana hukumomi dasu har sai sun biya albashi da sauran ababen more rayuwa.

DUBA WANNAN: An karbo biliyoyi daga kudaden da Abacha ya kai Turai

Hukumar ta NPC dai, ta fitar da wannan sabon adadi ne a ranar Talata a birnin New York na Amurka a wajen taro kan yawan mutane da ci gaba karo na 51. Shugaban hukumar kidayar Mr Eze Duruiheoma, ya ce a yanzu yawan al'ummar kasar ya kai miliyan 198, wato miliyan biyu ya rage ta kai miliyan 200.

Mista Duruiheoma ya ce ana hasashen cewa Najeriya za ta zama kasa ta uku da ta fi yawan al'umma a duniya nan da shekara 30 masu zuwa. Ya kara da cewa a shekaru 50 da suka gabata, yawan al'ummar mutanen da ke zaune a birane a kasra ya karu sosai ba tare da samun karin ababen more rayuwa da zai ishe su ba.

Matsin tattalin arziki ya jefa kasar da yan kasar mawuyacin hali, inda aka ga alkalumman tsaro da na laiffuka sun yi sama, sannan talauci da yunwa da fatara suka hau sama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng