Hukumar 'yansanda ta kama tare da sakin sunayen wasu 'yansanda, ta fadi laifukansu

Hukumar 'yansanda ta kama tare da sakin sunayen wasu 'yansanda, ta fadi laifukansu

Hukumar yan'sanda ta jihar Legas ta kama mutane biyar cikin kungiyar masu yaki da fashi da makami a ranar talata wadanda ake zargi da karbar cin hanci daga wani marubucin najeriya wanda suka tilasta da ya boye a bandakin banki.

Hukumar 'yansanda ta kama tare da sakin sunayen wasu 'yansanda, ta fadi laiukansu

Hukumar 'yansanda ta kama tare da sakin sunayen wasu 'yansanda, ta fadi laiukansu

A wata zantawa da kakakin rundunar yan'sandan ta jihar, Chike Oti, yace jami'an ance su zauna ne a Ipakodo amma ba Ikeja ba kamar yanda suka fada da farko.

A ranar talata ne PREMIUM TIMES ta ruwaito yanda James Ibe-Anyanwu, marubucin najeriya wasu jami'ai masu neman cin hanci suka tsare shi har tsawon awa hudu.

Mr. Ibe-Anyanwu, Dan kasuwa, mamallakin kamfani mai suna PLANEX, yace wai har takardun kamfani shi jami'an sun kwace.

Marubucin yaje bankin zenith da ke Ago-Palace way, okota, domin harkar kasuwancin shi. A lokacin ne wani jami'i ya sameshi inda suka rankaya gurin motarshi da bukatar ya nuna musu takardun shi. Bayan ganin takardun ne suka kira shi da Dan damfara kuma suka bukaci ya shiga motarsu suje ofishinshi dake Ikeja.

Suka ki sauraron rokonshi. A inda marubucin ya shige bandakin banki a tsammanin su ya shiga bankin ne don ciro musu kudi. Yayi amfani da wayar hannun shi yayi rubutu a shafin shi na Facebook a inda ya bayyana abinda ke faruwa dashi. Bayan awa hudu yan'sanda suka bayyana a gurin yayin da jami'an suka gudu.

Kwamishinan yan'sandar jihar Edgal Imohimi a take yayi umarnin nemosu, kamosu da zartar musu da hukunci. Kakakin rundunar yan'sandan yace a bincikensu sun gano kungiyar ta samu jagorancin Inspector Jude Akhoyemta na SARS, da ke Ikeja ne.

DUBA WANNAN: PAsto ya zargi matarsa da kwartanci

Kungiyar ta kunshi sifetoci guda biyu, Taiwo Omojope da Arigidi Ebibor da kuma sajan guda uku, Rotimi Adesoba, Olalekan olakunle da kuma Friday Oni. Har yanzu dai ana kan bincike a inda aka gano sifeta Jude Akhoyemta da aka ambata da farko bashi da laifi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel