Kotun Najeriya ta saki wasu mayakan kungiyar Boko Haram, ta dora laifin kan gwamnatin tarayya

Kotun Najeriya ta saki wasu mayakan kungiyar Boko Haram, ta dora laifin kan gwamnatin tarayya

Wata kotu a Abuja, ta saki wasu da ake zargin y'an kungiyar boko haram ne, da aka kama su shekara biyar da suka wuce. An sake su ne yau Laraba, bayan da alkaliyar kotun ta yi zargin jan-kafa a shari'ar su daga bangaren gwamnati.

Babbar kotu dake birnin tarayya Abuja, ta sallami mutane biyun da ake zargi, Ibrahim Ahmad da kuma Sani Argungu.

Mai shari'a Binta Nyako, ta gano cewa Malam Ahmad na tsare tun shekarar 2013 yayin da shi kuma Malam Argungu yake tsare tun 2012 ba tare da yi musu shari'a ba tun lokacin da aka kama su kawo yanzu, kuma ga shi bangaren gwamnati sun gaza gabatar da shaida kwakwara a kansu.

Kotun Najeriya ta saki wasu mayakan kungiyar Boko Haram, ta dora laifin kan gwamnatin tarayya

Wasu mayakan kungiyar Boko Haram

Sai dai mai shari'a Nyako ta ce, duk lokacin da masu kara daga bangaren gwamnati suka kawo shaidu, za'a iya sake kamo wadanda ake zargin. A dan haka ne ta ce, wadanda ake zargin, za'a cigaba da sa ido a kansu. Ta kuma gargade su da su guji mu'amala da mutanen da ba na kirki ba.

DUBA WANNAN: Buhari ya gana da wani babban malamin addinin Kirista a Landan, duba hotunansu

Malam Ibrahim wanda ma'aikacin tsaro ne a cikin gidan gwamnatin jahar Sokoto, ana zarginsa da bayar da bayanan sirri ga y'an kungiyar ta boko haram.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel