Buhari ya gana da wani babban malamin addinin Kirista a Landan, duba hotunansu

Buhari ya gana da wani babban malamin addinin Kirista a Landan, duba hotunansu

- A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya bar Najeriya zuwa birnin Landan na kasar Ingila gabanin wani taron kasashen shugabannin duniya na kungiyar “Commonwealth”

- A yau, Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin babban malamin addinin Kirista a kasar Landan, Akbishof Justin Welby

- Kafin ya bar Najeriya, shugaba Buhari, ya bayyana niyyar sa ta sake tsayawa takara, karo na biyu, a zaben shekarar 2019

A yau, Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin babban malamin addinin Kirista a kasar Landan, Akbishof Justin Welby, da jakadan Najeriya a kasar Ingila, George Adesola Oguntade, a gidan gwamnatin Najeriya dake kasar.

Buhari ya gana da wani babban malamin addinin Kirista a Landan, duba hotunansu

Hotunansu ganawar Buhari da babban malamin addinin Kirista a Landan

A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya bar Najeriya zuwa birnin Landan na kasar Ingila gabanin wani taron kasashen shugabannin duniya na kungiyar “Commonwealth” da za a yi daga ranar 18 zuwa 20 ga watan Afrilun da muke ciki.

DUBA WANNAN: Hotuna masu kayatarwa daga bikin cikar Dangote shekaru 61

A yayin ziyarar sa a kasar Ingila, shugaba Buhari, zai gana da Firaministan kasar Ingila, Theresa May, domin tattaunawa a kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Buhari ya gana da wani babban malamin addinin Kirista a Landan, duba hotunansu

Buhari ya gana da babban malamin addinin Kirista a Landan

Kafin ya bar Najeriya, shugaba Buhari, ya bayyana niyyar sa ta sake tsayawa takara, karo na biyu, a zaben shekarar 2019, batun da har yanzu ‘yan Najeriya ke cigaba da tofa albarkacin bakinsu a kai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shafe watanni yana zaman jinya a kasar Ingila shekarar da ta gabata, 2017.

Buhari ya gana da wani babban malamin addinin Kirista a Landan, duba hotunansu

Shugaba Buhari da Malamin addinin kirista daa jakadan Najeriya

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel