Masu garkuwa da mutane sun bindige wani dan kasar Syria har lahira a cikin birnin Kano

Masu garkuwa da mutane sun bindige wani dan kasar Syria har lahira a cikin birnin Kano

Wasu gungun masu garkuwa da mutane sun kashe wani mutumin kasar Syria mazaunin jihar Kano, Ahmed Abu Areeda, a birnin Kano tare da yin awon gaba da yaronsa mai shekaru 14, Muhammad Ahmed.

Daily Trust ta ruwaito yan bindigan sun kashe Ahmed ne a daren Talata 10 ga watan Afrilu, da misalin karfe 8:05 na dare, a farfajiyar ofishin kungiyar bada agaji ta Red Cross dake garin Kano, inda yaje ya dauki motarsa da ya ajiye.

KU KARANTA: Masana Ilimin Kimiyya sun gano kasar Sifaniya na girgiza a duk lokacin da Messi ya ci Kwallo

Sai dai a wannan lokaci, Ahmed yana tare da yayansa guda biyu, hakan ne yan bindigan yunkurin yin awon gaba da yayan duka biyu, inda shi kuma mamacin ya ja da yan fashin a kokarin da suke yi na sace yayan nasa.

Wani shaidan gani da ido ya shaida ma majiyar Legit.ng cewar yan bindigan sun kais u takwas, inda suka rabu gida biyu, yayin da wasu suka bi Ahmed har cikin farfajiyar Ofishin na Red Cross, wasu kuma suka dakata a waje, a cikin motarsy kirar Pijo, mai ruwan shudi, mai duhun gilasai.

Wadanda suka bi sawunsa zuwa ofishin ne suka bindige shi a kai, sa’annan suka tafi da yaronsa guda, yayin da dayan ya nemi mafaka ta hanyar tserewa, kamar yadda wani shaidan gani da idon na daban ya tabbatar.

An gano cewar mamacin, ya kwashe sama da shekaru 20 yana zama a jihar Kano, inda ya fara da aiki da kungiyar masu hada labulaye na Najeriya, a matsayin akawu na tsawon shekaru 10, bayan ya ajiye aikin ne kuma ya bude nasa kasuwancin a Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel