Mafi dadewa a kujerar Sanata ya samu karamcin majalisar Dattawa

Mafi dadewa a kujerar Sanata ya samu karamcin majalisar Dattawa

A yayin da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Alechenu Bonaventure Mark ya cika shekaru 70 a duniya a ranar yau ta Laraba, majalisar ta taya shi murna tare da karamci kasancewar sanata mafi dadewa a kujera ta majalisar.

Majalisar a cikin wasu sakonni na shafin dandalin sada zumunta ta twitter, ta yabawa tsohon shugabanta tare da mika lambar kasancewar sa Sanata mafi dadewa a kan kujejarar shugabancin ta bayan kafuwar kasar nan.

Sanata David Mark

Sanata David Mark

Shugaban majalisar na yanzu, Sanata Bukola Saraki, shine ya jagoranci wannan karamci tare da girmamawa da aka yiwa tsohon shugaban ta Sanata David Mark yayin taya shi murnar cikar sa shekaru 70 a duniya.

KARANTA KUMA: Amaechi ya bayyana ainihin albashin Ministocin Buhari

A yayin haka kuma Legit.ng ta tunatar da mai karatu cewa, a 'yan watannin da suka gabata ne hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta fara gudanar da wasu bincike kan tsohon shugaban majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel