An gurfanar da wani a kotu saboda cin zarafin wani dan Majalisa a kafar Facebook

An gurfanar da wani a kotu saboda cin zarafin wani dan Majalisa a kafar Facebook

Kwamishinan hukumar Yan sanda reshen jihar Akwa Ibom, Mr. Adeyemi Ogunjemilusi ya gurfanar da wani Emmanuel Udo dan asalin karamar hukumar Nsit Atai saboda laifin cin zarafin wani dan Majalisar Wakilan Tarayya mai wakiltan Uyo, Dr. Michael Enyong.

Jami'an hukumar Yan sandan farin kaya (DSS), Jami'an hukumar kiyaye sirrin kasa (NIA) da kuma jami'an hukumar Yan sandan Najeriya ne sukayi hadin gwiwa wajen kamo wanda ake tuhumar mai suna Udo.

An gano cewa Udo yana amfani da dandalin sadarwan na Facebook inda ya bude shafi na bogi da sunan Emem Etina kuma yayi ikirarin cewa dan Majalisar wato Dr. Enyong yayiwa wata Regina Christopher ciki a karamar hukumar Uyo.

An gurfanar da wani a kotu saboda cin zarafin wani dan Majalisa a kafar Facebook

An gurfanar da wani a kotu saboda cin zarafin wani dan Majalisa a kafar Facebook

DUBA WANNAN: An kashe wani dan kasuwar kasar Syria a Kano

Kwamishinan Yan sandan jihar ya gurfanar da Uyo a gaban kotu inda ake tuhumar sa da laifi guda na cin mutunci amma Udo bai amince da aikata laifin ba.

Lauya mai kare wanda aka gurfanar, Mr. Honesty Akpanam a ranar Laraba ya roki kotu sassauci kana ta bayar da belin Udo. An bayar da belinsa kan kudi N500,000 tare da mutum daya daya tsaya masa wanda dole ya kasance yana zaune kusa da inda kotun take.

A makonin da suka shude, an gano cewa Udo yayi amfani da wani hoto daya samo daga shafin WHO na wata mai ciki yar kasar Kamaru dake karbar maganin zazabin cizon sauro inda yace itace Regina Christopher da Enyong yayi wa ciki.

Bayannai sun nuna cewa sharin da Udo yayi wa dan majalisar ya janyo mutane da dama suna da yadda labarin inda suke Allah wadai da halin dan majalisar alhalin basu san sharri akayi masa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel