An gurfanar da wata a kotu bisa zargin kashe dan makwabciyarta ta hanyar tsafi

An gurfanar da wata a kotu bisa zargin kashe dan makwabciyarta ta hanyar tsafi

A yau Laraba ne aka gurfanar da wata mace mai shekaru 30, Princess Ofonome, a gaban alkalin kotun Mararaba da ke jihar Nasarawa inda ake zarginta da kashe yaron makwabciyarta ta hanyar tsafi.

Wanda ake tuhuma da ke zaune a Unguwar Kabayi, Mararaba a jihar Nasarawa ta musanta zargin aikata cin zarafi da kuma aikata kisa.

Mai shigar da kara, Hamen Donald ya shaidawa kotu cewa wata Juliet Joseph da ke zaune a unguwar Kabayi ne ta kawo kara ofishin Yan sanda na 'A' Division dake Mararaba a ranar 9 ga watan Afrilu misalin 11.00 na safe.

An gurfanar da wata a kotu bisa zargin kashe dan makwabciyarta ta hanyar tsafi

An gurfanar da wata a kotu bisa zargin kashe dan makwabciyarta ta hanyar tsafi

Yace mai wanda ta kawo koken ofishin Yan sandan tayi ikirarin cewa wanda ake tuhuma ne tayi sanadiyar rasuwar danta ta hanyar tsafi.

DUBA WANNAN: Dubi sunayen 'Yan sandan da suka garkame wani a bandakin banki saboda yaki basu cin hanci

"A ranar 5 ga watan Afrilu, wanda ta shigar da karar tana zaman makokin danta daya rasu watanni 2 da suka wuce, sai wanda ake tuhumar ta furta wasu kallamai da suka tabbatar da cewa ita ta kashe yaron ta kuma tana shirin kashe ta.

"Kalaman da ta furta sun hada, 'Duk kudan da bayya jin gargadi zai shiga kabari tare da gawa, kuma ciyawa basu gama fitowa a kabarin na farkon ba gashi na biyun na nan tafe.

"Wanda ake tuhumar kuma ta tafi bayan gida inda tayi ta fadin wasu surkulle, inda tayi amfani da yaji, man ja, albasa, da gishiri kuma ta zana wata yar da'ira da gawayi," inji Donald.

A cewar mai shigar da karar, abinda ta aikata ya sabawa doka fenal code kuma an tandar da hukuncin ga wanda suke aikata hakan a sashin na 397.

Alkalin kotun, Ibrahim Shekarau, ya bayar da belin wanda ake tuhuma kan kudi N50,000 tare da mutum daya da ya tsaya mata kana ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Afrilu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel