Jawabi daga shugaban OAU, kan Farfesa da ke lalata da 'yan mata don cin jarrabawa

Jawabi daga shugaban OAU, kan Farfesa da ke lalata da 'yan mata don cin jarrabawa

- Shugaban jami'ar Obafemi Awolowo ya nuna damuwarshi akan hirar wayar da ta bazu na wani farfesa a jami'ar da yake bukatar saduwa da wata daliba domin ta haye Jarabawar shi

- Dalibai da malaman makarantar wadanda suka ji hirar, sun sanar da PREMIUM TIMES cewa muryar Richard Akindele ce, farfesa a fannin Accounting a jami'ar. Malamin, wanda dalibar ta ambaci sunan shi a hirar dai har yau bai ce komai ba

Jawabi daga shugaban OAU, kan Farfesa da ke lalata da 'yan mata don cin jarrabawa

Jawabi daga shugaban OAU, kan Farfesa da ke lalata da 'yan mata don cin jarrabawa

A wata tataunawa,shugaban makaranta, Eyitope Ogunbodede yace a ranar laraba yasa hannu akan fara binciken domin gano ko ma waye. Yace abinda akayi ya sabawa dokar jami'ar.

Jami'ar ta hada kwamiti domin binciken zargin wanda zasu kammala a cikin sati daya. Duk wanda aka kama kuwa za a saba mishi.

Jami'ar bazata lamunci laifuka makamantan haka ba daga dalibai ko malaman ta.

Shugaban kungiyar malamai masu karantarwa na jami'ar, Niyi Sunmonu yace " in har aka tabbatar da cewa hirar gaskiya ce, to mai laifin bai cancanci zama a kowanne gurin koyarwa ba." ana tsammanin malamai dai harda gyaran tarbiyya sukeyi" inji malamin jami'ar.

DUBA WANNAN: 'Yar 17 ta kawo wa Najeriya yabo

Shugaban Educational Rights Campaign, Hassan Soweto, yayi Allah wadai da wannan abu, yace irin wadannan abubuwan da suka faru a jami'ar a baya ba a dau wani mataki a kai ba.

A wata hira da akayi da tsohon dalibin makarantar a Rave 91.7 FM, Osogbo, Frank Talk yayi kira da a samarda kungiya mai zaman kanta wacce ta hada da wakilai daga cikin malamai, dalibai da kuma kungiyoyin taimakon kai da kai na mata domin bincike.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel