An kama mutum 8 daga cikin garadan da ake zargi da kone wata yarinya bayan yi mata fyade

An kama mutum 8 daga cikin garadan da ake zargi da kone wata yarinya bayan yi mata fyade

'Yan sandan kasar Pakistan, a yau Laraba, sun yi nasarar cafke wasu mutane 8 da ake zargi da kone wata yarinya mai shekaru 8 bayan sun yi mata fyade.

A cewar 'yan sandan, yarinyar ta bar gida Lahadi domin sayen alawa daga wani shago dake daf da gidansu.

Bayan wasu sa'o'i sai aka samu yarinyar a wani kango tana hayaki, alamun an cinna mata wuta da ranta. Yarinyar ta mutu bayan jami'an 'yan sanda sun kai ta asibiti.

Jami'an 'yan sandan sun ce suna zargin an yiwa yarinyar fyade kafin daga bisani a kona ta duk da har yanzu ana dakon sakamakon binciken masana a kan gawar ta.

An kama mutum 8 daga cikin garadan da ake zargi da kone wata yarinya bayan yi mata fyade

Wata karamar yarinya da aka yiwa aure a kasar Pakistan

Batun fyade da kona yarinyar ya jawo barkewar zanga-zanga a kasar Pakistan daga daliban makarantu, lauyoyi, 'yan kasuwa, da Kungiyoyi daban-daban a birnin Chichawatni dake yankin Punjab.

Masu zanga-zangar na neman a tabbatar da yin adalci ta hanyar hukunta wadanda suka ci zarafin karamar yarinyar.

DUBA WANNAN: Kansila ya mutu ranar bikin taya shi murna

Jami'in hukumar 'yan sanda, Muhammad Amin, dake gudanar da bincike a kan laifin ya ce har yanzu suna jiran sakamakon likitoci a kan gawar yarinyar tare da bayyana cewar sun kama fiye da mutane 12 dangane da afkuwar lamarin.

Wani ma'aikacin asibitin dake gudanar da bincike a kan gawar yarinyar ya ce, fiye da kashi 70% na jikin yarinyar ya kone.

Ko a watan Janairu saida kisan wata yarinya mai shekaru 7 bayan anyi mata fyade, ya jawo barkewar zanga-zanga a birnin Kasur dake yankin na Punjabi kafin daga bisani a yankewa mutumin da ya aikata laifin hukuncin kisa.

Wata kungiya mai zaman kanta, Sahil, ta ce ana yiwa a kalla kananan yara 11 fyade kullum a kasar Pakistan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel