Mutane 257 sun hallaka a hatsarin jirgin saman soji a Algeria

Mutane 257 sun hallaka a hatsarin jirgin saman soji a Algeria

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 257 ne suka mutu sakamakon hatsarin jirgin sama a babban birnin kasar Aljeriya.

Jirgin wanda ke dauke da fasinjoji wanda mafi yawansu sojoji ne da iyalansu ya fadi ne jim kadan bayan ya tashi daga wani sansani.

Daga cikin mamatan akwai mutanen yankin Polisario 26 da ke samun goyon bayan gwamnatin Algeria wajen neman 'yancin cin gashin kai a yammacin Sahara daga Morocco.

Ma'aikatar tsaron Algeria ta tabbatar da rasuwan daukacin fasinjojin ba tare da samun mutun guda da ya kubuta da ransa ba.

Mutane 257 sun hallaka a hatsarin jirgin saman soji a Algeria

Mutane 257 sun hallaka a hatsarin jirgin saman soji a Algeria

Mataimakin Ministan tsaro na kasar, Janar Ahmed Gaid Salah da ya ziyarci yankin da lamarin ya faru, ya bukaci guanar da bincike kan hatsarin.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta kori karar da shugaban hukumar ‘Yan Sanda ya shigar a kan Majalissa

Tuni daruruwan motocin daukar mara lafiya da manyan motocin kashe gobara suka kama hanyar isa wurin da lamarin ya faru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel