Manyan Jami’o’in Duniya 19 sun yi wata ‘Yar Najeriya tayin karatu

Manyan Jami’o’in Duniya 19 sun yi wata ‘Yar Najeriya tayin karatu

- ‘Yar Najeriya ta samu damar yin karatu a manyan makarantun Duniya

- Oludamilola Adekeye ta samu damar shiga irin Jami’ar Yale da Columbia

- Baiwar Allah ta nuna bajinta a wajen karatun da tayi a baya na Sakandare

Mun samu labari daga Gidan labarai na CNN cewa Duniya akalla 19 ne su ka nemi wata ‘Yar Najeriya ta zo tayi karatu bayan tayi abin a yaba mata a lokacin da ta ke makarantar Sakandare a Kasar UAE.

Manyan Jami’o’in Duniya 19 sun yi wata ‘Yar Najeriya tayin karatu

An yi Oludamilola Oluwadara Adekeye tayin makarantu rututu

Manyan Jami’o’in da babu irin su a Duniya irin su Jami’ar Yale ne su ka ba Oludamilola Oluwadara Adekeye damar shiga Makarantun tayi karatun da ta ke so. Abin sha’awa shi ne shekarar wannan yarinya 17 kacal.

KU KARANTA: An nemi a Ma'aikatan Gwamnati su rika sa kayan gida

Bayan Jami’ar Yale akwai kuma wasu makarantu irin Jami’ar Stanford da Jami’ar Columbia da kuma Makarantar kasuwanci ta Landan da duk su ka ba wannan Hazika damar yin karatu ta goge da sauran ‘Dalibai a Duniya.

Oludamilola Oluwadara Adekeye ta samu damar shiga Jami’o’in Duniya. Idan da ta so shiga irin Jami’ar Yale da Columbia. Baiwar Allah ta nuna bajinta a wajen karatun da tayi a baya na Sakandare a lokacin tana karatu a Dubai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel