Wata Mata ta gurfana gaban Kuliya da laifin sace jaririya 'yar watanni 7 da haihuwa

Wata Mata ta gurfana gaban Kuliya da laifin sace jaririya 'yar watanni 7 da haihuwa

Mun samu rahoto da sanadin shafin PM News cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne wata mata Briget Haruna, ta gurfana gaban watan Kotu dake zaman ta a garin Abuja bisa laifin sace wata jaririya 'yar watanni bakwai da haihuwa.

Dalhatu Zannah, jami'in dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa kotun cewa, wani mutum mai sunan Vourjack Pam mazaunin unguwar Gwarimpa, ya yi korafin wannan mata a ofishin 'yan sanda na Life Camp tun a ranar 4 ga watan Afrilu.

Wata Mata ta gurfana gaban Kuliya da laifin sace jaririya 'yar watanni 7 da haihuwa

Wata Mata ta gurfana gaban Kuliya da laifin sace jaririya 'yar watanni 7 da haihuwa
Source: Twitter

Vourjack dai ya bayyana cewa, a yayin da mai dakin sa Misis Godiya ta je ziyarar duba mara lafiya a babban asibitin Gwarimpa tun a ranar 3 ga watan Afrilu, Bridget ta yaudare ta ta hanyar yin awon gaba da jaririyar ta.

KARANTA KUMA: Tsaro ya tsananta a yayin ci gaba da sauraron karar tsohon gwamnan jihar Katsina

Zannah ya ci gaba da cewa, wannan korafi ya sanya jami'an 'yan sanda suka bazama cikin bincike da har aka yi nasarar damko Bridget a unguwar Jabi dake kauyen Daki Biyu tare da wannan jaririya.

A yayin da wannan laifi ya sabawa sashe na 288 cikin dokar kasa, alkalin kotun Mista Abubakar Sadiw, ya bayar da belin Bridget akan kudi N50, 000 bayan ta gabatar da majinginanta har mutum biyu kuma ya daga sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Mayu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel