Masari ya bukaci masu kula da kudade na ma’aikatu dasu goyawa Buhari baya wurin yakar rashawa

Masari ya bukaci masu kula da kudade na ma’aikatu dasu goyawa Buhari baya wurin yakar rashawa

- Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bukaci masu kula da kudade na ma’aikatu a fadin kasar nan ta hanyar bayyana shuwagabannin ma’aikatu dake aikata rashawa

- Gwamnan yace ba yanda za’ayi shuwagabannin ma’aikatun su debi kudaden gwamnati ba tare da sanin masu kula da kudaden ma’aikatun ba

- Masari yace wannan aikin na yaki da rashawa a kasar na aiki ne wanda ya shafi kowa da kowa musamman masu kula da kudaden gwamnati

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, a ranar 10 ga watan Afirilu, 2018, lokacinda yake zantawa da NAN, ya bukaci masu kula da kudade na ma’aikatu a fadin kasar nan ta hanyar bayyana shuwagabannin ma’aikatu dake aikata rashawa.

Gwamnan yace ba yanda za’ayi shuwagabannin ma’aikatun su debi kudaden gwamnati ba tare da sanin masu kula da kudaden ma’aikatun ba.

Masari ya bayyana hakane a ranar Talata, lokacin da ya karbi bakuncin Alhaji Shehu Ladan, shugaban kungiyar masu kula da kudaden gwamnati na Najeriya, lokacin da suka kai masa ziyara a jihar Katsina.

Masari ya bukaci masu kula da kudade na ma’aikatu dasu goyawa Buhari baya wurin yakar rashawa

Masari ya bukaci masu kula da kudade na ma’aikatu dasu goyawa Buhari baya wurin yakar rashawa

Masari yace wannan aikin na yaki da rashawa a kasar na aiki ne wanda ya shafi kowa da kowa musamman masu kula da kudaden gwamnati na ma’aikatu.

KU KARANTA KUMA: Ministar Buhari ta yi karin haske kan badakalar kudaden Abacha

Ya kara karfafawa masu kula da kudaden gwamnati dasuyi iya bakin kokarinsu don ganin cewa an magance yawan satar kudaden gwamnati tare da cewa bukatar shugaba Buhari ce ta kokarin yaki da rashawa a kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel