Nigerian news All categories All tags
Jami’an EFCC sun damke yan damfara 4

Jami’an EFCC sun damke yan damfara 4

Jami’an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta yi ram da wasu yan damfaran yanar gizo 4 a ranan Asabar, 7 ga watan Afrilu 2018 a jihar Legas.

Yan damfaran sune, Ale Daniel, Tunde Badmus, Adams Tunde Adedeji da Ajiboye Gbenga.

An damke wadannan yan damfara ne a unguwan Lekki na jihar Legas kan laifin damfara ta yanar gizo. An bibiyesu ne bisa ga rahoton cewa suna rayuwa mai tsada ba tare da wani takamamman aikinyi ba.

Jami’an EFCC sun damke yan damfara 4

Jami’an EFCC sun damke yan damfara 4

Shugaban hukumar EFCC, shiyar jihar Legas, Akanninyene Ezima, ya yi kira ga masu gidaje su san mutanen da suke ba hayan gida kafin basu saboda gujewa fushin doka.

Za’a gurfanar da su a kotu muddin an karashe binciken da ake gudanarwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel