Kotu ta kori karar da shugaban hukumar ‘Yan Sanda ya shigar a kan Majalissa

Kotu ta kori karar da shugaban hukumar ‘Yan Sanda ya shigar a kan Majalissa

- Kotun Jabi a birnin tarayya ta kori karar da shugaban hukumar ‘Yan Sanda ya shigar game da hakkin dan adam

- Justice Abba Bello Mohammed ya bayyana haka lokacin da yake yanke hukunci a kan Majalissa na cewa sun keta hakkinsa na dan adam na kiranda sukayi

- Yace sashe na 88 da 89 na dokar kasa ya bawa Majalissa izinin bincikar duk wata matsala kuma ta kira kowane mutum don ta bincikeshi

Kotun Jabi a birnin tarayya ta kori karar da shugaban hukumar ‘Yan Sanda, Ibrahim Idris, ya shigar game da keta hakkin dan adam da ya shigar akan majalissa.

Justice Abba Bello Mohammed ya bayyana haka lokacin da yake yanke hukunci a kan Majalissa na cewa sun keta hakkinsa na dan adam na gayyatar da kwamitinsu sukayi masa.

Yace sashe na 88 da 89 na dokar kasa ya bawa Majalissa izinin bincikar duk wata matsala kuma ta kira kowane mutum don ta bincikeshi.

Kotu ta kori karar da shugaban hukumar ‘Yan Sanda ya shigar a kan Majalissa

Kotu ta kori karar da shugaban hukumar ‘Yan Sanda ya shigar a kan Majalissa

Alkalin ya yanke hukunci tun bayana karar da Idris ya shigar ta hanyar Dr Alex Izinyon (SAN), inda ya bukaci a cigaba da sauraron karar kafin a yanke hukunci, kafin 1 ga watan Fabrairu da aka gama shari’ar.

KU KARANTA KUMA: Ministar Buhari ta yi karin haske kan badakalar kudaden Abacha

IGP Idris yayi karar shugaban majalissar dattijai, Bukola Saraki, tare da Sanata Hamman Isa Misau; Francis Alimikhena; Binta Masi Garba; Suleiman Hunkuyi; Duro Faseyi Samuel; Ogba Joseph Obinna; Nelson Effiong; da kuma Abdulaziz Nyako, game da keta masa hakkinsa na dan adam.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel