Mutane 8 sun shiga hannu da laifin fyade 'yar shekara 8 kuma suka ƙone ta da ran ta

Mutane 8 sun shiga hannu da laifin fyade 'yar shekara 8 kuma suka ƙone ta da ran ta

A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar 'yan sanda ta kasar Pakistan, ta cafke wasu miyagun mutane 8 da ake zargin su da ƙone wata yarinya 'yar shekara 8 da ran ta bayan sun fyade ta, inda wannan lamari ya janyo zanga-zanga a kasar.

A cewar hukumar 'yan sanda, wannan yarinya dai ta bar gidansu da tsakar ranar Lahadin da ta gabata domin sayen kayan tantande irin na yara a wani shago daura da gidan su, inda bayan awanni sai tsinto ta aka yi a wani kaurataccen gida da konuwa a wasu sassa na jikin ta.

Legit.ng ta fahimci cewa, an garzaya da wannan yarinya asibiti cikin gaggawa inda anan ta ce ga garinku nan.

Rahotanni da sanadin shafin jaridar PM News sun bayyana cewa, anyi lalata da wannan karamar yarinya kafin a cinna ma ta wuta kamar yadda bincike 'yan sanda ya tabbatar.

KARANTA KUMA: Jerin Kasashe duniya da ba bu hukunci ga wadanda suka aikata Fyade

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, dalibai daga makaratu na matakai daban-daban sun shiga cikin sahun zanga-zangar da aka gudanar akan manyan hanyoyin kasar domin nuna rashin goyon bayansu akan lamarin tare da neman adalci ga wannan yarinya da ta riga mu gidan gaskiya.

A yayin haka kuma, a watan Janairun da ya gabata ne aka zartar da hukuncin kisa kan wani matashi da laifin kashe wata yarinya 'yar shekara 7 bayan ya fyade ta a garin Kasur na kasar Pakistan.

A cewar wata kungiya mai zaman kan ta a garin Sahil mai kare hakkin yara ta bayyana cewa, a duk kwanan duniya akan samu kimanin kanann yara 11 da aka ketawa haddi a kasar ta Pakistan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel