Nigerian news All categories All tags
Bamu son Buhari: Yan zanga-zanga sun mamaye gidan gwamnatin Najeriya a Ingila

Bamu son Buhari: Yan zanga-zanga sun mamaye gidan gwamnatin Najeriya a Ingila

Fusatattun yan Najeriya sun mamaye gidan gwamnatin Najeriya dake Landan inda shugaba Muhammadu Buhari ke zaune tun da ya tafi kasar Birtaniya ranan Litinin, 9 ga watan Afrilu, 2018.

Masu zanga-zanga dauke da takardu sun nuna rashin jin dadinsu da gwamnatin shugaba Buhari. Kamar yadda suka rubuta kan takardun hannunsu, sun yi kira da shugaba Buhari ya kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a jihar Benuwe da sauran sassan Najeriya.

Wasu yan zanga-zanga sun caccaki shugaba Buhari a kan alanta niyyar sake takara zaben 2019 duk da gajiyarwarsa a karon farko na mulki.

Bamu son Buhari: Yan zanga-zanga sun mamaye gidan gwamnatin Najeriya a Ingila

Bamu son Buhari: Yan zanga-zanga sun mamaye gidan gwamnatin Najeriya a Ingila

An yi zanga-zangan sun yi ne cikin lumana tsare da jami’an yan sanda.

Amma fadar shugaban kasa ta ce wasu masu fama da rashawa ne suka shirya wannan zanga-zanga saboda tsoron takaran shugaba Buhari.

KU KARANTA: Malaman makaranta 200 sun shiga taksu

A ranan Litinin, shugaba Buhari ya bayyanawa kwamitin masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC cewa zai sake takara kujeran shugaban kasa a 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel