Nigerian news All categories All tags
Jonathan ya gargadi matasa da kada su kara maimaita kuskuren da sukayi a baya na zaben shuwagabanni

Jonathan ya gargadi matasa da kada su kara maimaita kuskuren da sukayi a baya na zaben shuwagabanni

- Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya shawarci matsan Najeriya musamman jogororin cikinsu akan kada su maimaita kuskuren da sukayi a baya wurin zaben shuwagabanni

- Jonathan ya bayyanawa kungiyar New Najeriya 2019 da ta kwararrun matasan Najeriya, lokacin da suka kai masa ziyara birnin Yenagoa

- Yayi jinjina ga matasan game da kokarin da sukeyi na kawo wani sabon cigaba a siyasar Najeriya

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya shawarci matsan Najeriya musamman jogororin cikinsu akan kada su maimaita kuskuren da sukayi a baya wurin zaben shuwagabanni.

Jonathan ya bayyanawa kungiyar New Najeriya 2019 (NN-2019) da ta kwararrun matasan Najeriya, lokacin da suka kai masa ziyara birnin Yenagoa, a jiya.

Jonathan ya gargadi matasa da kada su kara maimaita kuskuren da sukayi a baya na zaben shuwagabanni

Jonathan ya gargadi matasa da kada su kara maimaita kuskuren da sukayi a baya na zaben shuwagabanni

Jonathan yayi jinjina ga kungiyar matasan, wadda Chima Nwafor da Moses Siasia ke jagoranta, game da kokarin da sukeyi na kawo wani sabon cigaba a siyasar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Tafiyan Landan: Dalilin da yasa Buhari bai rubuta wasika ga majalisar dokoki ba

Tsohon shugaban kasar ya bayyana kungiyar matasan a matsayin wata Katanga ko garkuwa ta al’umma, kuma duk wanda ke son cigaban al’umma dole ne ya girmama matasa, saboda ko a tarihi matasa sune suka taka muhimmiyar rawa a mulkin Najeriya tun farkonsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel