Nigerian news All categories All tags
2019: Sule Lamido ya tafi neman tabarraki a wajen IBB a wata ziyara da ya kai masa (Hotuna)

2019: Sule Lamido ya tafi neman tabarraki a wajen IBB a wata ziyara da ya kai masa (Hotuna)

A yayin da zabukan 2019 ke kara karatowa, yan siyasa masu neman dafe madafan iko sun fara tattara jama’a tare da neman hadin gwiwa da abokan siyasa, da kuma binciken kofofin da nasara zata samu.

A irin haka ne aka hangi keyar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido a fadar tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB, kamar yadda Rariya ta ruwaito.

KU KARANTA: Barayin shanu dauke da muggan makamai sun kai hari a jihar Kaduna, sun jikkata mutane 3

2019: Sule Lamido ya tafi neman tabarraki a wajen IBB a wata ziyara da ya kai masa (Hotuna)

Ziyarar

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Lamido ya kai wannan ziyara ne a ranar Talata 10 ga watan Afrilu, inda ya samu IBB a gidansa dake saman Dutse, a birnin jihar Neja, wato Minna.

Bayan da kyakkyawar tarba da tsohon shgaban kasa IBB yayi wa Sule Lamido, a yayin tattunawarsu ma yayi masa fatan alheri da samun nasara a takarar da ya shiga na shugaban kasa a zabukan 2019.

2019: Sule Lamido ya tafi neman tabarraki a wajen IBB a wata ziyara da ya kai masa (Hotuna)

Ziyarar

Idan za’a tuna, tun a shekarar data gabata ne dai Sule Lamido ya bayyana maitarsa a fili game da burinsa na darewa kujerar shugaban kasar Najeriya, ta hanyar kawar da gwamnatin Buhari a zaben 2019, sakamakon gazawar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayyana, a cewar Lamidon.

2019: Sule Lamido ya tafi neman tabarraki a wajen IBB a wata ziyara da ya kai masa (Hotuna)

Ziyarar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel