Nigerian news All categories All tags
Amaechi ya bayyana ainihin albashin Ministocin Buhari

Amaechi ya bayyana ainihin albashin Ministocin Buhari

Da sanadin jaridar The Punch, mun samu rahoton cewa Babban Ministan Sufuri na kasa Mista Rotimi Amaechi, ya bayyana ainihin albashin sa da cewar yana daukan N950, 000 a kowane watan duniya kuma da wannan albashi yake biyan bukatun sa.

Ministan ya yi wannan fashin baki a yayin halartar taron kaddamar da wani littafi mai taken Dignity Service wanda tsohon ministan harkokin kasashen ketare ya wallafa, Marigayi Dakta Matthew Mbu.

Ministan Sufuri; Rotimi Amaechi

Ministan Sufuri; Rotimi Amaechi

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin gudanar da wannan taro ne babban limamin Cocin Katolika ta Abuja, John Cardinal Onaiyekan ya bayyana cewa, akwai damuwa yadda dattawa ke ci gaba da mulkar kasar nan a madadin su mika akalar mulki a hannun matasa.

KARANTA KUMA: Majalisar Kasar Somaliland ta zartar da dokar daukan fyade a matsayin laifi

Babban limamin ya ci gaba da cewa, tsaffin shugabannin irin su; Cif Obafemi Awolowa, Nnamdi Azikiwe da kuma Abubakar Tafawa Balewa, sun taka rawa gani ne a kasar nan sakamakon kasancewar matasa a yayin da suke rike da akalar mulki.

Ya kara da cewa, irin wannan yanayi ya sanya aka zabi mawallafin wannan littafi Marigayi Mbu a matsayin Minista tun yana matashi dan shekara 23 a duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel