Nigerian news All categories All tags
2019: Da za’a dora Buhari a sikeli bai cancanci a sake zabarsa ba - Farfesa Moghalu

2019: Da za’a dora Buhari a sikeli bai cancanci a sake zabarsa ba - Farfesa Moghalu

- Idan muka tattara hankali wuri guda muka yiwa gwamnatin Buhari duba na tsanaki, zamu ga cewa bai cancanci a sake zabarsa ba

- Ni ina da manufofin da zasu fitar da kasar daga halin kuncin da take ciki na tabarbarewar tattalin arziki da kuma sha'anin tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari na cigaba da fuskantar adawa daga mutane da dama, amma sukar tayi zafi ne tun bayan da ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a 2019.

Idan da za’a dora Buhari a sikeli bai cancanci a sake zabarsa ba - Farfesa Moghalu

Shugaban kasa Muhmmadu Buhari

Daga cikin wadanda ke adawa da yunkurin na Shugaba Buhari har da Farfesa Kingsely Moghalu, tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya wato CBN. Inda Moghalun yake cewa da za’a dora Buharin a sikeli da tabbas nauyinsa bai kai a sake zabarsa a karo na biyu ba.

Idan da za’a dora Buhari a sikeli bai cancanci a sake zabarsa ba - Farfesa Moghalu

Frafesa Kingsely Moghalu

Tsohon mataimakin gwamnan bankin da ya tsunduma siyasa kuma har yake shirin yin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019, ya bayyana cewa, "Magana ta gaskiya, indai za'ai la’akari da irin cigaban da Shugaba Buharin ya kawo ne to tabbas bai cancanci a kara zabarsa a karo na biyu ba."

Maganar tasa dai ta biyo bayan bayyana kudirinsa a sake tsayawa takara da shugaba Muhammadu Buhari yayi. Farfesa Kingsely Moghalu yace, bai kamata a sake zabarsa Muhammadu Buharin ba, duba da cewa, a yanzu Najeriya ce kasar da tafi kowacce kasa yawan matalauta a duniya ga hauhawar farashi da kimanin 15% da kuma cigaban tattalin arzikin kasar nan da kullum yake tafiyar hawainiya da kasha 1% saboda rashin sanin makama.

KU KARANTA: 2019: Matasa na goyon bayan Buhari game da sake tsayawa takara

La’akari da haka, tabbas ya kamata a samu sauyi a shugabancin kasar, muna bukatar shugaban da zai tafi da kowa ba wariya a cikin mulkinsa ya kuma hada kan duk yan Najeriya kana ya bullo da tsare-tsaren da zasu fitar da mutane daga talauci. A cewar Farfesan

Moghalu, mai aniyar tsaya takarar shugabancin kasar nan, yanzu haka yana kasar Amurka, inda yake tattaunawa da yan Najeriya mazauna kasashen waje, domin lalubo mafita akan yadda gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaza fitar da kasar nan daga cikin halin ni yasu, kuma har Buharin yake yunkurin sake tsayawa takara domin zarcewa a 2019.

"A halin da muke ciki na karuwar talauci da kuma tabarbarewar tsaro, Ni ina mai tabbatar muku da cewa, ina da kudirori da manufofin da zasu fitar da kasarmu daga cikin wannan hali da muke ciki gami da tafiya tare da kowa da samar da cigaban da zai daga martabarmu a idon duniya a wannan karni na ashrin da daya." A cewar Farfesa Moghalu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel