Nigerian news All categories All tags
Tafiyan Landan: Dalilin da yasa Buhari bai rubuta wasika ga majalisar dokoki ba

Tafiyan Landan: Dalilin da yasa Buhari bai rubuta wasika ga majalisar dokoki ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba rubuta wasika ga majalisar dokoki ba kan tafiyarsa zuwa kasar Ingila, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A zaman majalisa jiya, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya karanta wasiku hudu daga shugaban kasa, banda guda daya kan tafiyarsa zuwa kasar Ingila.

A baya Buhari ya yi rubutu ga majalisar dokoki kamar yadda sashi 145 na kundin tsarin mulkin 1999 ta tanadar.

Shugaban kasar ya bar kasar a ranar Litinin zuwa kasar Ingila sannan ana sanya ran zai kasance a chan har zuwa ranar 20 ga watan Afrilu.

Tafiyan Landan: Dalilin da yasa Buhari bai rubuta wasika ga majalisar dokoki ba

Tafiyan Landan: Dalilin da yasa Buhari bai rubuta wasika ga majalisar dokoki ba

Wata majiya ta kusa da shugaban majalisar dattawan ta bayyana wa majiyarmu cewa shugaban kasar ba rubuta wasika ga majalisar dokoki domin sanar masu da tafiyarsa ba.

“An karanto wasiku hudu daga shugaban kasar a majalisa. Banyi tunanin ya aika ko wacce wasika akan tafiyarsa ba,” cewarsa bayan ya bukaci a boye sunansa.

KU KARANTA KUMA: Ma’aikatan barayin gwamnati ne ke zanga-zanga a Ingila – Fadar shugaban kasa

Amma wata majiyar tace babu bukatar shugaban kasar ya rubuta wasika ga majalisa akan ziyaran.

“Ba hutu ya tafi ba. Idan kun karanta sanarwar hadiminsa da kyau, ya nuna cewa zai tafi ziyarar aiki ne don haka, babu bukatar ya rubuta ko wani wasika,” cewar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel