Nigerian news All categories All tags
Ma’aikatan barayin gwamnati ne ke zanga-zanga a Ingila – Fadar shugaban kasa

Ma’aikatan barayin gwamnati ne ke zanga-zanga a Ingila – Fadar shugaban kasa

- Ofishin shugaban kasa yace wasu data bayyana a matsayin Barayin gwamnatin Najeriya sun shirya hanyar batawa Buhari ziyarar da zaya kai kasar London

- Ofishin yace barayin gwamnanti da masu aikata rashawa a kasar sunyi hayar mutane wadanda zasuyi zanga-zanga idan shugaba Buhari ya isa garin London

- Babban gurinsu shine don su lalata tsare-tsaren da Buhari yayi a zuwansa Ingila

Ofishin shugaban kasa, a ranar 10 ga watan Afirilu, a birnin tarayya ya bayyana, cewa wasu data nuna a matsayin Barayin gwamnatin Najeriya sun shirya hanyar batawa Buhari ziyarar da zaya kai birnin Landan.

Ofishin a ranar Talata, ya bayyanwa mai kawo rahoto na fadar shugaban kasa, cewa barayin gwamnanti da masu aikata rashawa a kasar sunyi hayar mutane wadanda zasuyi zanga-zanga idan shugaba Buhari ya isa garin London.

Babban gurinsu shine don su lalata tsare-tsaren da Buhari yayi a zuwansa Ingila, bai wuce awowi 24 ba, bayan Muhammadu Buhari ya bayyana kudirinsa na sake tsayawa takarar shugaban kasa a Najeriya, barayin gwamnatin da masu aikita rashawar suka shiga rudu.

Ma’aikatan barayin gwamnati ne ke zanga-zanga a Ingila – Fadar shugaban kasa

Ma’aikatan barayin gwamnati ne ke zanga-zanga a Ingila – Fadar shugaban kasa

Daya daga cikin masu zanga-zangar yace babu ja da baya akan zuwansu wurinda za’a gudanar da taron shuwagabannin kasashe na CHOGM.

KU KARANTA KUMA: Bamu razana da tsayawar Buhari takara ba - Magoya bayan Atiku

Babban mataimakin shugaban kasa ta fannin labaru da harkokin jama’a, Malam Garba Shehu, yace masu wannan zanga-zangar bazasu hana shugaba Buhari aikata abunda ya kaishi kasar ta UK, ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel